Da yawa mutane sun dauka cewa, canji shi ne, a sauya shugaba, wanda hakan shi zai kai mutanen kasa zuwa ga gyaran al’umma, wasu kuma sun fahimci canji shi ne, kame wadanda suka aikata barna. Ko a tunaninsu wani mutum kadai shi zai kawo canji cikin al’umma.
Hakan sai ya sanya yanzu hira a majalisu ba ta wuce ta zagin shugabanni ko la’antarsu, duk wai da sunan sun gagara wajen kawo sauyi, ko sun jefa mutane a bala’i, ko wai har yanzu ai ana kisa. Na’am, Mutane sun manta da abubuwa guda uku kamar haka:
1- Allah Kadai ke samar da canji ba mutum ba, budi da kunci duk na gare Shi, Shi kadai ba hannun wani dan Adam . Himma da dabara da karfi da wayo ba su kawo canji, dukkan su sabubba ne kawai. Allah Kadai ke kawo canji.
2- Canji ba ya samuwa idan ku al’umma ba ku canja aniyar ku da halin ku ba. Misali a nan; kai dan kasuwa ne, me ka bari daga cin riba ko ruwa?
Kai ma’aikacin gwamnati ne, ta yiwu kai akawun kudi ne, ko shugaban makaranta (Head-master), ko malamin makaranta, ko shugaba a wani bangare, ko lebura a wata ma’aikata, ko yaro a gurin ubangidansa, ko maigida ne kai da yara a kasanka. To, ya ya kai ka canja cikin cuwa-cuwar aikinka ko wata almundahana?
3- Ba a samun canji ba tare da an gyara kofofin barna ba, wannan kuwa dole ya sa a ji jiki ko yaya yake, kafin abin ya mike.
Sanin kowane an zauna shekaru 16 cikin barna a wannan kasa, kisa ya zama ruwan dare, cin hanci ya mamaye kowane ofis, karya da yaudara su ne tamburan da yawa daga cikin shugabanni, danne marar karfi da zalunci su ne kwalliyar shugabanni. Kowane shashasha sai ya zo ya yi abin da ya ga dama, ko da sunan shugabanci ko addini ko wakilci. To, shin ta ya ya dare guda za a wayi gari a ga an samu sauyi?
Ko kun manta gwamnatin da ta shude, ana kasheku, amma ba sa jajanta muku? Wani lokacin da ake kasheku din ma a daidai lokacin suna can suna rawa akan munbarin siyasa. Kun manta suna kallo ana kwace shanunku duk da haka cikinsu babu wani mai hankalin da yake tausaya muku?
Wajibi ne kowa ya gyara kura-kuransa, ya gyara mu’amalarsa, ya nesanci barnar da yake yi, sannan ya yi wa shugabanninsa addu’a. Domin Ahmad bin Hambal cewa ya yi: “Da ina da wata addu’ar da na san karbabbiya ce a gun Allah, da shugabana zan yi wa”. Imam Buhari yake cewa: “An umarce mu da mu yi musu addu’ar gyaruwa, ba a umarce mu da mu yi musu addu’ar halaka ba! matukar suna nan a matsayinsu na shugabanninmu ko da sun yi zalunci sun ketare iyaka”
Idan ka ga mutum yana yi wa shugaba addu’ar halaka, to ma’abocin son zuciya ne. Idan ka ga yana yi musu addu’ar shiriya to ma’abocin sunna ne insha Allah”.
Kowa ya sani cewa: Lallai Allah Ba ya sauya halin da mutane ke ciki, har sai sun sauya da kansu,” kamar yadda Alkur’ani ya tabbatar mana.Sai mu kara kokarin kawo canji mai ma’anta, tare da neman taimakon Allah, ta hanyar yi wa kawunanmu addu’ar alkairi da neman shiriyar shugabanninmu.
Muhammad Muhammad Abubakar ya rubuto daga Sakkwato 08053151313
Sai mutum ya canza zai ga canji
Da yawa mutane sun dauka cewa, canji shi ne, a sauya shugaba, wanda hakan shi zai kai mutanen kasa zuwa ga gyaran al’umma, wasu kuma…