✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sai mun wulakanta Gwamnonin da suke rike albashi- NLC

Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta ce, zata hada gwiwa da kungiyar ‘yan kasuwa ta duniya ITUC don fallasa sunayen Gwamnonin da ke rike wa…

Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta ce, zata hada gwiwa da kungiyar ‘yan kasuwa ta duniya ITUC don fallasa sunayen Gwamnonin da ke rike wa ma’aikatansu albashi da kuxaxen fansho na watanni ba biya.

Shugaban kungiyar NLC Ayuba Wabba, ne ya bayyana hakan yayin taron shekara na kungiyar ‘yan fansho na Najeriya  NUP a Abuja.

Kungiyar NLC ta ce zata baiwa ma’aikata umarni a tashoshin jiragen saman Najeriya da su dakatar da duk wani tsohon Gwamna da ake bi bashin albashi tare da wulakanta shi  a tashar, yayin da yake shirin fita daga Najeriya zuwa kasar waje.