✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Sai mun rage ma’aikata mu iya biyan albashin dubu 30’

A ranar Larabar da ta gabata ce Gwamnonin Najeriya suka bukaci Kungiyar Kwadago ta zabi daya tsakanin biyan Naira dubu 30 mafi karancin albashi ko kuma…

A ranar Larabar da ta gabata ce Gwamnonin Najeriya suka bukaci Kungiyar Kwadago ta zabi daya tsakanin biyan Naira dubu 30 mafi karancin albashi ko kuma rage ma’aikata a duk fadin kasar nan.

Wannan sanarwa na kunshe ne cikin wata takardar bayan taro da kungiyar gwamnonin ta fitar a Abuja. Takardar ta bayyana cewa abu ne maras yiwuwa ga dukkan jihohin kasar nan su biya dubu 30 mafi karancin albashi, sai dai idan ma’aikatan zasu amince da a rage yawansu ko kuma gwamnatin tarayya ta duba yiwuwar kara haraji a kasar nan.

A yayin da yake karanta takardar, Shugaban Kungiyar Gwamnonin, Alhaji Abdul’aziz Yari ya ce, “Babu wata mafita illa aiwatar da dayan abubuwa biyu. Ko dai a rage ma’aikata ko kuma a kara batun haraji. A yanzu haka kungiyarmu ta gwamnoni ta kafa wani kwamiti wanda zai gana da shugaban kasa a ci gaba da neman bakin zaren warware wannan takaddama ta karin albashi”

Tun a baya dai babban kwamitin hadin gwiwa da aka kafa don duba wannan batu da kungiyar kwadagon ke bukata na karin albashin ya amince da biyan dubu 30 mafi karancin albashi a maimakon dubu 55 da kungiyar kwadagon ta nema tun farko.