✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Sai mai kudi zan aura wa uwata ‘yar shekara 60’

Wani saurayi mai suna Ajibade Adedapo, na nema wa mahaifiyarsa mai shekaru 60 mijin da ai aure ta. Adedapo wanda ya dora hotunan mahaifiyar tasa…

Wani saurayi mai suna Ajibade Adedapo, na nema wa mahaifiyarsa mai shekaru 60 mijin da ai aure ta.

Adedapo wanda ya dora hotunan mahaifiyar tasa ‘yar shekara 60 ya bar mutane cikin al’ajabi musamman yadda ya hakikance cewar sai mai arziki zai aura mata.

“Ina nema wa mahaifiyata mai shekaru 60 abokin zama… Idan kana da mahaifi da matarsa ta rasu ko suka rabu amma mai dukiya…. Ku tuntube ni, zan iya zama agolanku,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter @ajibade_adedapo

Wannan haja da ba a taba gani ko jin irinta ba ta ja hankali mutane da dama wanda akalla fiye da mutum dubu biyu suka duba.

Sai dai wasu da suka leka hajar mahaifiyar tasa sun yi watsi da sharain da matashin ya gindaya na cewar atafau sai sai kudi tunda ai hali ma jari ne.

Wasu kuma na ganin yana da gaskiya ya nema wa mahaifiyarsa mai dukiya idna za ta huta.

%d bloggers like this: