Hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC ta ɗage zaɓen gwamna da ɗan majalisar jiha a akwatuna 10 dake Legas zuwa ranar Lahadi.
Kwamishinan INEC a jihar Legas Olusegun Agbaje ne ya sanar da ɗage zaɓen da yammacin Asabar .
Ya ce ɗagewar ta shafi mazaɓu biyu dake Victoria Garden City a ƙaramar hukumar Eti-Osa.
Ya ƙara da cewa jami’an zaɓen da aka tura yankin ne suka ƙi gudanar da aikinsu saboda fargabar ƙalubalen da suka fuskanta a lokacin zaɓen shugaban ƙasa.
“Don haka an ɗage gudanar da zaɓen sai gobe Lahadi da ƙarfe 8:30 na safe”.