✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sai kowa ya taimaka a yaki da jabun kayayyaki – Hukumar SON

 Dokta Paul Angya shi ne Mukaddashin Daraktan Hukumar da ke Tabbatar da Ingancin Kayayyaki wato Standards Organisation of Nigeria (SON). Aminiya ta gana da shi…

 Dokta Paul Angya shi ne Mukaddashin Daraktan Hukumar da ke Tabbatar da Ingancin Kayayyaki wato Standards Organisation of Nigeria (SON). Aminiya ta gana da shi game da aikace-aikacen hukumar da dai sauransu. Ga yadda hirar ta kasance:

 

Aminiya: Akwai maufofin da aka kafa wannan hukuma da su, ko jama’a suna maraba da ayyukan wannan hukuma?
Eh, zan iya cewa ’yan Najeriya suna karbar ayyukan wannnan hukuma da hannu biyu-biyu. Kuma ayyukanmu ba su takaita ga ’yan Najeriya kawai ba, saboda gaba daya jama’ar duniya ne muke wa hidima. Ayyukan wannan hukuma ya hada da tabbatar dg Muqaddashin Daraktan Hukumar da ke Tabbatar da Ingancin Kayayyaki (SON), Dokta Paul Angya ingancin kayayyaki, wannan kuma wani abu ne da dan Adam ya ba fifiko tun fil’azal. Duka wadanda suka san Hukumar SON sun san cewa tana aiki ne don ta inganta rayuwarsu. Kuma na san cewa kowane dan Najeriya yana kaunar ingantattun kayayyaki.

Aminiya: Me  za ka ce game da kayayyakin jabu da suka cika kasar nan, kuma wane sako hakan ke isarwa game da nasarorin da kuke ikirarin kuna samu?
Akwai abubuwa biyu a nan: Idan aka yi magana yawaitar jabun kayayyaki, hakan ba ya nufin wata gazawa ba ce daga bangaren hukumar. A wasu kasashen da suka ci gaba, ba a samun irin wadannan hukumomi. Jama’a ne da kansu suke guje wa kayayyakin bogi, suna neman ingantattu. Amma a nan nahiyarmu ta Afirka muna da karancin ilimi da fahimta. Abu na biyu shi ne: a wasu lokuta sai an tilasta wa jama’a amfani da ingantattun kaya. Kuma yana da kyau a fahaimci cewa galibin kayyakin jabu ba a nan kasar ake kera su ba, shigo da su ake daga ketare. Ka ga ke nan akwai bukatar a inganta tsaro akan iyakokinmu na ruwa. Kuma ’yan Najeriya ne suke shigo da wadannan kayayyakin. A har kullum burinmu shi ne ya zama kowane kaya da ke Najeriya ya zama ingantacce.
Akwai kalubalen da muke fuskanta musamman don mukai matsayin da za mu tsaya sosai don yaki da wannan matsalar da gurbatattun kayayyaki a kasar nan.  Ba a jin duriyarmu a tsakankanin kasashe takwarorinmu. Wani kalubale da kuma muke fuskanta shi ne na karancin ma’aikata saboda ma’aikatanmu ba su wuce dubu biyu ba. Kuma ana bukatarmu ne da mu karade duka fadin kasar nan. Ayyukanmu ya hada da kowane bangare na rayuwa, bangaren lafiya ne, na’urori ne, kayan abinci ne, wayoyin lantarki ne, kayan gini ne da dai sauransu.

Aminiya: Ta wace hanya ce mutanen gari za su iya taimaka muku wajen yaki da irin wadannan jabun kayayyakin?
Mutane za su iya taimaka mana wajen sayan kayayyakin da suke ganin sun tabbatar da ingancinsu.

Aminiya: Ta yaya za su gane ingantattun kayayyaki?
Akwai wadansu tambari da ake sanya wa a jikin ingantattun kayayyaki kamar na NIS da sauransu alamomi. Kodayake, wannan wani abu ne da ya ta’allaka ga wayayyu jama’a. Wadanda ba su irin wannan basirar ta gane gurbatattun kaya, kamata ya yi su yi tambaya. Amma kuma koda sai bayan da mutum ya sayi kayan ne ya fahimce cewa kayan jabu ne, to sai ya mayar wurin da ya saya, idan kuma wanda ya sayar masa ya ki amsa, to don Allah mutum ya kai koke a ofishinmu mafi kusa da shi. Muna da ofisoshi a jihohi 36 da ke kasar. Abin da jama’a yakamata su fahimta shi ne babu wajibci a kan amfani da jabun kayayyaki, koda ko bayan mutum ya saye su ne. Doka ta ce zai iya mayar da shi wurin da ya saya don neman ingantacce. A kasar nan, mun saba idan mutum ya saye jabun kaya, yakan jefar da shi ne, ko kuma ya yi amfani da shi bisa tilas, amma a wasu kasashen duniya mayar da irin wadannan ake wurin da aka saya don neman sauyi. Batun gaskiya shi ne Sai kowa ya taimaka a yaki da jabun kayayyaki a kasar nan.

Aminiya: Me ye kake ganin ya sa aka ce Hukumar SON ta janye daga tashohin jiragen ruwan kasar nan?
Ba maganar wani laifi da hukumar ta aikata ba ne. Akwai dai bukatar saukaka matakan shigo da kayayyaki kasar kamar yadda  sauran takwarorinmu suke yi. Wannan ne ya sa, kuma ina ganin kowace kasa tana so ta yi cinikanyan da ’yar uwanta cikin sauki, kuma ba ta tare da wani bata lokaci ba. Ana ganin kasancewar Hukumar SON a tashoshin ya jawo tsaiko wajen fito. Har ila yau, rashin tantance ingancin kayayyaki ya sa masa’antunmu na cikin shiga sun mutu, ga matsalar rashin aikinyi a tsakankanin matasanmu da durkushewar tattalin arziki da sauransu. Kuma kamar yadda muke magana da kai, yanzu muna cikin zamanin ci gaban kwamfuta ne, za a iya wadannan ayyukan tantance kayayyaki cikin sauki idan aka tafi da zamani.