✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sai kin nuna min ubana —’Ya ga uwarta a kotu

Mutumin ya ce sam ba ’yarsa ba ce, domin bai taba kusantar mahaifiyarta, wadda tsohuwar matarsa ce ba

Wata mata ta maka mahaifiyarta a kotu tana neman sai ta nuna mata mahaifinta, a yankin Babban Birnin Tarayya.

Matar ta ce ta garzaya kotu ne bayan kannenta da suke zaune a tari sun matsa cewa dole sai ta fice daga gidan mahaifinsu, bisa hujjar cewa ita ba ’yar cikinsa ba ce.

Ta bayyana hakan ne a yayin zaman kotun da ke sauraron shari’ar a yankin Bwari, inda aka ci gaba da shari’ar a ranar Talata.

A yayin zaman kotun, mahaifiyar mai karar ta gabatar da wani mazaunin unguwar Dutsen Alhaji da cewa tsohon mijinta ne kuma mahaifin ’yar da ta haifa masa, kafin daga bisani iyayenta suka aurar da ita ga sabon mijinta.

Sai dai shi mutumin ya ce allambaram ba ’yarsa ba ce, domin bai taba kusantar mahaifiyarta, tsohuwar matar tasa ba.

Bayan sauraron bangarorin, alkali Abdurrahman Ibrahim ya ba da umarnin a yi wa tsoffin ma’auratan gwajin kwayar halitta (DNA) domin tabbatar da ikirarin kowannensu.

Ya kuma umarce su da cewa su biyun ne za su biya kudin gwajin da za a yi musu N200,000, sannan ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 8 ga watan nan na Agusta.