✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sai an biya N314,000 kafin mu duba ’yan Arewan da ’yan IPOB suka raunata – Likitoci

Likitocin dai sun ce ba za su taba majinyatan ba muddin ba a ajiye musu kudin ba.

Likitoci a wani asibitin mai zaman kansa a Garin Okigwe, na Karamar Hukumar Okigwe a Jihar Imo sun ki karbar wasu daga cikin mutum biyu da ’yan kungiyar ’yan awaren Biyarafa ta IPOB suka harba.

Likitocin dai sun ce ba za su taba majinyatan ba muddin ba a ajiye musu kudi Naira 314,000 ba.

Rahotanni sun ce majinyatan dai na cikin wadanda aka harba a kauyen Anayara, a cikin makon nan, kuma suka samu mummunan rauni, har daya daga cikinsu hanjinsa fito, dayan kuma ya samu karaya a hannunsa.

Hassan Abdullahi Sadik, wani mazaunin Okigwe ya shaida wa Aminiya cewa, “Lokacin da ’yan IPOB suka harbe mutanen a kauyen Anayara, sojoji ne suka dauko su suka kawo su asibitin mai zaman kasa, amma likitocin suka ki kulawa da su har sai an basu kudin da suka fada.

Ya ci gaba da cewa sai da sojojin suka sanya baki cewa su duba su za a biya su kudin sannan suka yarda suka duba wanda hanjin nasa ya fito, nan ma sai da ’yan uwansa suka fara kawo N50,000.

Hassan ya kuma ce likitocin sun ce iya kudin aikinsu suka caza, idan sun gama kuma majinyatan ne za su ci gaba da sayen magani

“Wanda ya sami karaya mai suna Bashir Muntari, likitocin sun ce sai an ajiye musu N100,000 kafin su taba shi. Shi kuma wanda hanjin cikinsa ya fito, suka ce sai an basu N214,000 kafin  su yi masa aiki,” inji Hassan.

Idan za a iya tunawa, a farkon makon nan wasu da ake zargin ’yan IPOB ne suka kashe mutum takwas ’yan Arewa a sassa daban-daban na Jihar Imo.