✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sahabbai Goma ’yan Aljannah (4)

Sayyidina Aliyu (RA) ya halarci dukan yake-yaken daukaka Musulunci tare da Annabi (SAW) in ban da Yakin Tabuka. Domin shi Manzon Allah (SAW) ya sanya…

Sayyidina Aliyu (RA) ya halarci dukan yake-yaken daukaka Musulunci tare da Annabi (SAW) in ban da Yakin Tabuka. Domin shi Manzon Allah (SAW) ya sanya Magajin Gari, ya bar shi a Madina

A Yakin Badar, Sayyadina Aliyu (RA), ya nuna jarunta kwarai domin ya ragargaji makiya Allah yadda ya kamata. Shi ne ya fara fita karon fito-na-fito (mubaraza) daga rundunar Musulmi. Daga cikin jimillar mutane saba’in da aka kashe a bangaren kafiran Makka, Sayyadina Aliyu (RA) ne ya kashe mutum 21 daga ciki. A Yakin Uhudu kuwa, yana cikin wadanda Allah Ya tabbatar da duga-dugansu, babu gudu, babu ja-da-baya. A wannan yaki sai da aka yi masa sara 16.

Haka Sayyadina Aliyu (RA) ya ci gaba da nuna jarunta da fatattaka gayyar tsiya ta kafirai a Yakin Gwalalo (Khandak) da sauran yake-yaken daukaka Musulunci da Musulmi. Duk kafirin da suka yi gaba-da-gaba da shi, sai ya aika da shi barzahu, don haka kafirai ke tsoron karo da shi.

Sayyadina Aliyu (RA), shi ya zama Halifan Manzon Allah (SAW) na hudu, bayan Sayyadina Usmanu (RA). An yi masa caffa (mubaya’a) a Masallacin Manzon Allah (SAW) ranar Juma’a 25 ga Zul- Hajji, Hijira na da shekara 35 (24 ga Yuni 656 Miladiyya).

Sayyadina Aliyu (RA), bai samu damar fita yake-yake a wajen, don fadada daular Musulunci a lokacin Halifancinsa ba. Domin ya karbi Halifanci, a wani mawuyacin lokaci kwarai, wanda ke cike da rigingimun cikin gida. Masamman sabanin ra’ayi da aka samu a tsakaninsa da Sayyadina Mu’awiyya dan Abu Sufyan (RA), Gwamman Sham, wanda ya kai ga aukuwar Yakin Basasa. Ga kuma tarzomar Hawarijawa (Khawarij) su kimanin mutum dubu 12 wadanda asali, cikin rundunar Sayyadina Aliyu (RA) suke, daga baya suka dauki tsattsauran ra’ayi game da addini, har ta kai, sai da Sayyadina Aliyu (RA), ya yake su, ya watsa taronsu.

Halifancin Sayyadina Aliyu (RA) na shekara hudu da wata tara, ya yi shi a lokacin fitinu da tawaye da tashe-tashen hankula wadanda suka barke a cikin gida. Wannan zai nuna mana irin dauriyarsa da himma, gami da jarunta, marasa misaltuwa. Fasaharsa ta kara fitowa fili a wannan lokaci. Domin irin dogayen hudubobi na yanke hanzari da ya rika yi bisa manyan al’amura a wurare daban-daban abin sai dai a yi shiru. Haka nan zurfin tunani, gami da tarin ilimi da Allah Ya ba shi, duk sun kara bayyana a wannan lokaci.

Sayyadina Aliyu (RA), ya rasu bayan jinyar kwana uku, sakamakon sararsa da takobi da wani gyauron Khawarijawa, Abdurrahman bin Muljam, ya yi ranar 27 ga Ramadan, Hijira na da shekara 40 da asuba, yayin da ya fito, yana kiran Sallah. Ya rasu yana da shekara 63 a duniya (Allah Ya kara masa yarda).

5. Dalhatu bin Ubaidullahi (Allah Ya yarda da shi):

“Wanda duk ke son ganin shahidi yana tafiya da kafafunsa to, ya dubi Dalhatu dan Ubaidullah” – (Manzon Allah SAW).

Shi ne Dalhatu dan Ubaidullahi dan Usmanu dan Amru dan Ka’abu dan Sa’adu dan Tanimu dan Muratu. Bukarashe, Bataiyime. Ana yi masa lakabi da “Dalhatu Khairi.”

Yana daga cikin Musulman farko, wadanda Sayyadina Abubakar (RA) ya kira su zuwa ga Musulunci. Ya yi musu jagora zuwa wurin Manzon Allah (SAW). Ya dandani irin azabar da kafiran Makka suka rika gana wa sahbban Manzon Allah (SAW) na farko. Yayin da ya musulunta shi da Sayyadina Abubakar (RA) sai Naufal dan Khuwailad ya kama su, ya hada su wuri guda, ya daure da kakkarfar igiya, ya tsire su, wai don kada su yi Sallah da zuwa wurin Manzon Allah (SAW). Allah Ya kara musu yarda.

Manzon Allah (SAW) ya hada Sayyadina Dalha da Zubairu dan Awwam a matsayin ’yan uwa, kafin yin hijira zuwa Madina. Yayin da Musulmi suka yi kaura zuwa Madina sai Manzon Allah (SAW), ya hada su ’yan uwantaka (shi Dalha) da Abu Ayyuba, mutumin Madina, (mai masaukin Manzon Allah na farko).

Sayyadina Dalhat yana daga cikin sahabban Annabi Goma da aka yi wa bushara da gidan Aljanna. Yana daga cikin mutum shida da Halifa Umar (RA), ya yi wasiyyar su yi shawara, su zabi Halifa a tsakaninsu. Shi ne kuma wanda Sayyadina Umar (RA) ya sanya ya yi wa mutane limanci, yayin da dan Banajusiya, Abu lu’ulu’atu ya soke shi a masallaci.

Bai samu halartar Yakin Badar ba, domin a lokacin Manzon Allah (SAW) ya tura shi kasar Sham, shi da Sa’idu dan Zaidu (RA) domin nemo labarai da sirrin abokan gaba. Amma ya halarci Yakin Uhudu da dukan yake-yaken da aka yi bayansa. Ya kuma halarci caffar yarda (Bai’atur Ridwan) ya ragargaji kafirai sosai a Yakin Uhudu ya kare Manzon Allah (SAW) da ransa, ya rike kibiyoyi da aka harbor wa Annabi (SAW) da hannunsa, har sai da yatsunsa suka shanye, aka kuma sare shi a ka a cikin wannan hali ya dauki Manzon Allah (SAW) a bayansa, ya hau dutse da shi (Allah Ya kara yarda a gare shi).

Sayyadina Dalhatu (RA) ya ce: “A Yakin Uhudu Manzon Allah (SAW) ya kira ni “Dalhatul Khairi” (tafiya) Yakin Tabuka kuma ya kira ni “Dalhatul Fayyad” (Maikwaranyar da alheri). A Yakin Hunainu kuwa, ya kira ni “Dalhatul Judu” (Dalhatul Baiwa). Aliyu dan Abu Talib ya ce! “Kunnuwana sun ji Ma’aikin Allah (SAW) yana cewa: “Dalhatu da Zubairu, makwabta ne a Aljanna.”

A wani Hadisin kuma Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda duk ke son ganin shahidi yana tafiya da kafafunsa to, ya dubi Dalhatu dan Ubaidullah.”

Sayyadina Dalhatu (RA) ya rasu, yana da shekara 60, ko 62 a zamanin Halifanci Sayyadina Aliyu (RA), (Allah Ya kara masa yarda).

6. Zubairu bin Awwam

“Kowane Annabi yana da Hawariyawa, Ni Bahawariyena, shi ne Zubairu dan Awwamu: –  (Manzon Allah SAW)

Shi ne Zubairu bin Awwam bin Khuwailidu dan Asad dan Abdu Uzza dan Kusayyu Ba’assade. Mahaifiyarsa kuwa, ita ce Safiya ’yar Abdul Mudallib, Gwaggon Manzon Allah (SAW), shi dan uwan Nana Hadiza ce (RA), matar Annabi (SAW). Ana yi masa alkunya da Baban Abdulahi.

Ya musulunta, bayan lokaci kadan da musuluntar Abubakar (RA), yana da shekara goma sha biyar. Shi ne wanda ya fara zare takobi don yaki saboda Allah, yayin da ya ji an ce kafiran Makka sun kama Manzon Allah (SAW). Saboda wannan, Manzon Allah (SAW) ya yi masa addu’a, shi da takobinsa.

Manzon Allah (SAW) ya hada su ’yan uwantaka shi da Abdullahi dan Mas’udu (RA) a Makka, yana cikin Musulmi farko da suka yi kaura zuwa kasar Habasha. Yayin da Musulmi suka yi hijira zuwa Madina kuwa, Manzon (SAW) ya hada shi ’yan uwantaka da Salamatu dan Salamatu dan Wak’shu, mutumin Madina.

Daga Aliyu dan Abu Dalib (RA), ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce “Kowane Annabi, yana dab Hawariyawa. Ni Bahawariyena, shi ne Zubairu dan Awwamu.”

Abdullahi dan Umar (RA) ya ji wani mutum yana cewa: “Ni ne dan Bahawariye. “Sai ya ce da shi: “Idan dan Zubairu ne kai, to shi ke nan, idan kuwa ba dansa ba ne to karya kake yi.”

Sayyadina Zubairu (RA) ya halarci Yakin Badar, yana sanye da wani rawani mai launin fatsi-fatsi. An ce Mala’ikun da suka halarci wannan yaki suna sanye ne da rawani irin na Sayyadina Zubairu (RA0, mai launin fatsi-fatsi. Haka kuma ya halrci dukan yake-yaken Musulunci tare da Annabi (SAW) kamar Yakin Uhudu da na Gwalalo da Sulhun Hudaibiyya da Yakin Khaibara da na Bude Makka da Yakin Hunainu da na Da’ifa, ya kuma halarci yakin Bude Birnin Misra, a zamanin Halifa Umar (Radiyallahu Anhu).

 

Imam Ahmad Adam Kutubi,

Nigeria Police Force,

Zone 7, Police Headkuarter,

Abuja. 08036095723