✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Safiyyah Jibril Abubakar: Mafaka ga marayun Najeriya

Safiyyah Jibril Abubakar ta shahara wajen rubuce-rubuce da tallafa wa marayu

Ma’abota kafofin sadarwa na zamani sun fi sanin Safiyyah Jibril Abubakar da suna Ummu-Abdoul.

Ta shahara da rubuce-rubuce, kama daga kagaggun labarai zuwa wasu batutuwa da suka shafi rayuwar al’umma, musamman mata.

A shekarar 2018 ma gajeren labarin da ta kago ya ciri tuta a Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Mata ta BBC Hausa, Hikayata, inda ya zo na daya.

Labarin ya yi Magana ne a kan wata budurwa da aka tilasta wa auren wani bawan Allah da bai san mutuncin mahaifiyarsa ba, balle na wata, daga bisani ya sake ta a kan dalilin da bai taka kara ya karya ba.

Labarin ya haska yadda al’umma ke yi wa matan da aurensu ya mutu kallon ’yan iska, ko da kuwa suna da kamun kai.

Daga karshe, kamar yadda Safiyyah Jibril Abubakar ta nuna, idan suka jure, suka jajirce, komai kyama, komai tsangwama, mata za su iya zama ababen misali.

‘Mu koma gona’

Wani abin ban sha’awa game da Tauraruwar tamu shi ne, duk da wadannan rubuce-rubuce da ma nasara da ta yi a gasar rubutu, ba adabi ta karanta ba.

Ta yi karantunta a matakin gaba da sakandare a fannin Ilimin Aikin Gona – har digiri na biyu ma ta yi a fannin Kimiyyar Kasar Shuka.

A yanzu haka kuma, malama ce a Sashen Ilimin Aikin Gona a Kwalejin Fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya, a jihar Kaduna.

Baya, goya marayu

Baya ga rubuce-rubucen da ta yi da dama, galibi a intanet, Ummu-Abdoul ta kuma kafa wata gidauniya don tallafa wa marayu da marasa galihu.

Gidauniyar, mai suna Nisaau Ahlil Jannah Charity Foundation, ta dauki nauyin karatun yara marayu da dama a wasu daga cikin jihohin Arewa.