Abin da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa, sai dai ga Saddam Sale Abubakar wani matashi dan kimanin shekara 22, haifaffen garin Kode da ke yankin karamar Hukumar Dawakin Kudu a Jihar Kano abin ba haka yake ba, kasancewar duk da yanayin tawayar halitta da yake da ita na kasancewarsa mai kafa daya, amma hakan bai hana shi yin fice a harkar wasan kwallon kafa ba, domin a yanzu haka shi ne mai tsaron ragar kungiyar wasan kwallon kafa ta FC Silber Boys Kode a garin Kode, wanda kuma saboda kwarewarsa da wuya ake iya sanya kwallo a cikin ragarsa. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana cewa babu nakasasshe sai kasasshe, ba a maraya sai rago.
Daga Lubabatu I. Garba, Kano
Aminiya: Muna son sanin tarihin rayuwarka a takaice?:
Saddam: An haife ni a shekarar 1994 a garin Kode a yankin karamar Hukumar Dawakin Kudu cikin Jihar Kano. Na yi karatun firamare da na sakandare duk a garin Dawaki a karamar Hukumar Dawakin Kudu. A yanzu haka ina kartun koyon malanta (NCE) a Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi inda nake karantar sashen tsimi da tanadi.
Aminiya: Ya aka yi ka fara wasan kwallon kafa?
Saddam: Tun ina karami nake sha’awar wasan kwallon kafa. Duk da cewa na taso a cikin yanayin lalura na gurguntaka wanda ya same ni tun ina dan watanni 18 da haihuwa, ya kasance da na dan fara tasowa sai nake shiga cikin yaran ’yan uwana a unguwarmu muna wasan tare da su, su kuma yaran sukan ba ni kwarin gwiwa wajen yin wasan. Tun ina yi kadan-kadan har Allah Ya sa aka yi min kafa wacce nake amfani da ita. Muna nan muna wasa sai muka bude fili a bayn gidan burodi. Daga baya sai muka koma wani fili da ake kira Eleben bullet.
Daga nan sai muka koma Kode United. Daga baya da muka girma sai muka bude fili namu na kanmu wato FC Silber Boys Kode. Ada ina shiga cikin fili a buga wasa tare da ni, daga baya kuma sai na fara tsaron gida. Ina yi yau da gobe sai abokan wasana suka fuskanci cewa na fi basira a bangren tsaron raga sai suka mayar da ni can.
Yanzu ta kai ma na fi jin dadin harkar tsaron raga fiye da buga wasan. Idan muka je wurin gasar wasanni kwallon kafa a wurare da dama idan mutane suka gani ni a mai tsaron raga sai ka ji mutame suna murna cewa za su iya cin kwallo sosai, sai kuma idan an shiga fili sai su ga al’amarin ba haka ba ne.
A kullum na kan samu kwarin gwiwar yin wasa idan ina ganin manyan ’yan wasa da ke burge ni wadanda suka hada da ’yan kulob din Kano Pillars (Masu gida) haka kuma ’yan kulob din Arsenal na Ingila suna burge ni.
Aminiya: Wane nasarori ka samu a harkar wasan kwallon kafa?
Saddam: Babu shakka ina kallon ficen da na yi, muna samun nasara a yawancin gasar wasannin kwallon kafa da ake hada wa a yankunan garuruwanmu. Mun yi wani gasa a garin Makole inda muka buga tsakaninmu da garuruwan Zogarawa da Gano da Wudil inda muka dauki kofi bayan ta kai mu ga fanareti. Haka kuma mun samu nasara a wasan da muka buga a garin Yankatsari da dorayi inda muka yi nasara. Haka kuma mun yi wasa da ’yan Kura inda muka samu nasara akansu. Haka kuma mun yi wasa da ’yan Tamburawa mun yi nasara akansu.. Haka kuma a lokuta da dama idan muka je wasa mutane sukan yi mini kyaututtuka don kansu ganin yadda nake gudanar da aikina na mai tsaron raga a matsayina na gurgu.
Aminiya: Wane kalubale kake fuskanta a rayuwa?
Saddam: Bababn kalubalen da muke fuskanta shi ne rashin abin hannu. A lokuta da dama muna so mu je wasu wuraren mu yi wasa amma saboda rashin kudi hakan ba ta samuwa.
Aminiya: Menene burinka a rayuwa?
Saddam: Burina na zama fitaccen dan wasan kwallon kafa a duniya. Ta bangaren karatu kuma ina so na yi karatu har na kai matsayin Dokta na ilimi.
Aminiya: Wane kira kake da shi ga gwamnati da kuma matasa, musamman wadanda ke da lalura irin taka?
Saddam : Ina kira ga gwamnatin Knao ta taimaka wa masu kwallon kafa, musamamn yanzu da ya zama yana daga cikin abubuwan da ake samun kudi da shi. Haka kuma wasan kwallon kafa yana sa mutum ya zama nagari a ciin al’umma, domin a lokuta da dama sakamakon suna son su yi suna ba sa aikata ayyukan badala don gudun bacin suna, don haka idan aka samu gwamnati na tallafawa harkar abubuwan rayuwar matasa za su inganta.
Ta bangaren matasa masu bukata ta musamman kuwa ina kira gare su da su zama masu dogaro da kansu, su daina bara. Duk da cewa kafa daya gare ni ban taba yin bara ba. Ba na sha’awarta kuma ba na fata na yi bara anan gaba. Kin ga bayan kasancewata dalibi nakan yi sana’ar wanki da guga a ranakun karshen mako don samun abin da zan dogara da kaina. Lokacin da gwamnatin Jihar Kano ta hana bara ba karamin farin ciki na yi ba, domin babu abin da bara ke haifarwa sai kashe zuciya. Hausawa ma sun ce ba nakasasshe sai kasasshe.