✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Daliban Kankara: Kungiyar Gwamnoni ta kai wa Masari ziyara

Gwamnoni sun bayyana takaici game da matsalar tsaro a Najeriya

A ranar Laraba, 22 ga Dasimba, 2020, Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta ziyarci Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari don jajanta masa kan dabdalar da aka sha gabanin ceto Daliban Makarantar Kimiyya ta garin Kankara.

Da ya ke jawabi bayan ganawarsu da Masari, Shugaban NGF, Gwamna Kayode Fayemi na Jiyar Ekiti, ya ce kungiyar na cike da takaicin yanayin tsaro a Najeriya.

Ya ce, “Mun tsinci kanmu a cikin taraddadi amma tabbas a yanzu mun gode wa Allah wanda da kudirarSa an ceto dukkan daliban da aka sace ba tare da wata matsala ba.

“Sai dai duk da haka, muna cike da damuwa game da matsalolin tsaro da suka addabi yankin Arewa maso Yamma da kuma Najeriya baki daya.

“Yanzu wannan matsala ta zama lamarin da ke aukuwa yau da kullum kuma Gwamnoni suna ci gaba da fadin-tashin ganin an bai wa wannan batu na matsalar tsaro fifiko duba da yadda ya mamaye kasarmu.”

Fayemi ya jinjina wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari dangane da jajircewarsa da kuma gudunmuwar da ya bai wa Gwamnatin Jihar Katsina da sauran masu ruwa da tsaki wajen ganin an ceto daliban na Makarantar Kankara cikin salama.

Gwamnonin da suka ziyarci Masari sun hadar da Shugaban Kungiyar, Kayode Fayemi na Jihar Ekiti; Muhammadu Badaru Abubakar na Jigawa; Aminu Waziri Tambuwal na Sakkwato; da takwaransa na Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu.