A ranar Litinin ne wata sabuwar zanga-zanga ta barke a Khartoum, babban birnin kasar Sudan.
Sai dai ’yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sanya kwalla wajen tarwatsa daruruwan masu zanga-zangar.
Ga dukkan alamu, tsugune ba ta kare ba a rikicin siyasar kasar Sudan, inda masu bore ke ci gaba da nuna adawa ga gwamnatin, bisa zargin sojoji ne ke jan ragamar kasar a fakaice.
Duk kuwa da mika mulki ga Fira Minista Abdallah Hamdok da Janar Abdel Fattah Al-Burhan wanda ya jagoranci juyin mulkin ya yi.
Bukatar masu boren ita ce su ga an mika ragamar mulki gaba daya a hannun farar hula ba tare da yin raba daidai da sojoji ba.
Amma bisa dukkan alamu abin kamar da wuya ganin jajircewar masu zanga-zangar da kuma cijewar sojojin da ke cikin gwamnatin wucin gadin.
A karshen watan Nuwamba ne aka cimma wata yarjejeniya tsakanin bangaren farar hula dana sojojin kafin mika mulki ga Hamdok.
A watan Oktoban 2021 ne aka yi zanga-zanga mafi girma a kasar saboda tsadar rayuwa da al’ummar kasar ke ciki, wanda hakan ya kai ga hambarar da gwamnatin farar hula ta kasar da dakarun soji suka yi.