✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabon rikici ya barke a Legas

Ana harbe-harbe da kone-kone a yankin Alaba Rago bayan barkewar rikicin.

Ana harbe-harbe bayan barkewar wani rikici a safiyar Litinin a yankin Alaba Rago da ke kan Babbar Hanyar Legas zuwa Badagry a Jihar Legas.

Mazauna sun ce wasu fusatttun mutane sun fito kan tituna suna tayoyi , yayin da ake ta jin rugugin harbi a yankin da ke kusa da Jami’ar Jihar Legas (LASU).

Wasu majiyoyi sun ce lamarin ya samo asali ne bayan sa-toka-sa-katsi tsakanin kungiyar direbobi ta NURTW da masu haya da babura a yankin.

Lamarin dai ya jefa mazauna cikin halin dar-dar, a yayin da aka rufe kofar shiga Jami’ar, wadda ta bukaci dalibai da ma’aikata su ci gaba da kasancewa a cikin harabarta.

Shaidu sun ce, jami’an tsaro na kokarin shawo kan lamarin, kamar yadda bidiyon lamarin da ke yawo a shafukan sada zumunta suka kuma tabbatar.