✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun kashe ’yan bindiga 4 a Imo

Ana zargin IPOB ta kashe mutum hudu tare da sake kona caji ofis a Imo

Jami’an ’yan sanda sun bindige maharan haramtacciyar kungiyar IPOB a sabon harin da ta kai a Jihar Imo.

’Yan bindigar da ake zargin mayakan kungiyar ne sun kona ofishin ’yan sanda na Izombe da ke Jihar.

Jami’in Hulda da ’Yan Sanda na Jihar Imo, Bala Elkana, ya ce, “Zugar tasu ta kai hari caji ofis na Izombe amma jami’an ’yan sanda suka fatattake su, suka kashe hudu daga cikinsu, ragowar kuma suka tsere da raunin harbi.”

Elkana ya kara da cewa an kai harin ne tsakanin karfe 7 zuwa 10 na dare ranar Asabar.

Ya ce an ci gaba da bin sawun maharan domin kamo su su fuskanci hukunci.

Harin ’yan bindigar na zuwa ne awanni kadan bayan farmakin da ake zargin kungiyar ta kai caji ofis din Atta a Karamar Hukumar Njaba ta Jihar.