✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon ma’aikacin BBC ya zama shugaban gidan rediyon Kwankwasiya

Tsohon ma'aikacin BBC, Dakta Maude Rabi'u Gwadabe ya zama shugaban sabon gidan rediyon Kwankwasiyya a Kano

Sabon gidan rediyon da kungiyar magoya bayan akidar Kwankwasiyya suka kafa a Kano ya nada fitaccen dan jarida kuma tsohon ma’aikacin BBC, Dokta Maude Rabi’u Gwadabe a matsayin shugabansa.

Gidan rediyon na Nasara Radio zai rika yada shirye-shirye a kan mita 98.5 a zangon FM kuma tuni ya karbi lasisin fara watsa shirye-shirye daga Hukumar Kula da Kafafen Watsa Labarai ta Kasa (NBC).

Nasara Radio mallakin tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ce.

Bayanin nadin Maude na kunshe ne a sanarwa da Jami’in Gudanarwa kuma Sakataren Kwamitin Tsare-tsaren tashar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne a ranar Litinin.

“Mun kafa gidan rediyon Nasara ne domin yada manufofin cigaban al’umma ta hanyar shirye-shirye da labarai na gaskiya kuma da dumi-dumi.

“Muna alfahari da samun gogaggun ma’aikata da za su tafiyar da tashar. Dakta Maude zai kasance mai matukar amfani tasha ‘yar yayi irin ta Nasara a karni na 21.

“A madadin mai wannan tashar da kuma Kwamitin Gudanarwarta, muna taya shi murna”, inji sanarwar.

Shi dai Daka Maude na da kwarewa a bangaren aikin jarida da kuma karantar da shi, kuma ya yi aiki a wurare da dama ciki har da Kamfanin jaridar Triumph, gidan rediyon Freedom da sashen Hausa na BBC da kuma Jami’ar Bayero da ke Kano.

A shekarar 2019 ya ajiye aiki da jami’ar kan radin kansa inda ya koma wallafa wata jarida ta shafin intanet mai suna Kano Focus.

Kafin nadin nasa dai ya kasance mai kwararren mai aikin tuntuba kan harkokin watsa labarai ga kungiyoyi da dama a Najeriya.

Jihar Kano dai ta yi fice wajen tarin kafafen watsa labarai musamman na rediyo.