Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya ce sabon filin jiragen dakon kaya na kasa sa kasa da ke Damaturu zai fara aiki ranar Juma’a 29 ga watan Mayu.
Da yake ran gadin sabon filin saukar jirgi mai saukar ungulun da ya gina a Damaturu, gwamnan ya ce filin jiragen dakon kayan zai fara ne da gwajin saukar jirage.
A cewarsa gwamantinsa za ta gina barikin sojin sama tare da samar da wadattun kayan aiki a filin jirgin domin tabbatar da aiki yadda ya kamata.
- El-Rufa’i zai daure iyayen yaran da ke bara
- Na samu duk alherin da ake samu a waka —Maryam Fantimoti
Mai Mala Buni ya bayyana haka ne a sadda Kwamandan Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya, Air Marshal Sadiq Abubakar da ke ziyarar gani da ido a filin jirgi mai saukar ungulun da gwamnatinsa ta gina.
Ya kuma yaba da goyon bayan da Gwamnatin Tarayya da sojoji da jam’ar jihar suke bayarwa a yaki da ta’addanci a jihar Yobe.
A jawabinsa Air Marshal Sadiq ya yaba da yadda gwamnan ke kokarin samar wa rundunar da kyakkyawan yanayin aiki.
“Na ji dadi da gwamna ya ba mu wurin girke kayan aiki da sojojinmu da ke yaki da jihar Yobe.
“Na tabbata hakan zai sa mu yi saurin tunkarar duk wata matsalar tsaro daga cikin jihar Yobe, sabanin daga Maiduguri,” inji shi.