Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta ce zaben 2023 yana cikin dalilan da suka sa Gwamnatin Tarayya ta dakatar da yunkurinta na janye tallafin mai.
Ministar, wacce take jawabi yayin taron Ministocin Kudi na nahiyar Afirka da kuma Bankin ba da Lamuni na Duniya (IMF), ta kuma ce tuni gwamnatin ta cire tallafin lantarki, inda ta ce yanzu na man ta sa a gaba.
- Za a fara musayar dalibai tsakanin makarantar jikan Inyass da ta Izala a Zariya
- An sake sace mutum 15 a kauyen Zamfara
Sai dai ta ce annobar COVID-19 da zaben 2023 mai zuwa ne suka taka musu birki daga cire tallafin.
A cewar Ministar, “Muna nan muna shirin cire tallafi, amma mun fuskanci koma-baya; a da shirinmu shi ne mu cire shi nan da watan Yuli Mai zuwa, amma ga zabe na tunkarowa, sannan ba a gama murmurewa daga COVID-19 ba, shi ya sa muka ja da baya.
“Amma mun samu nasarar cire tallafin lantarki salim-alim, ba tare da mutane sun lura ba, maganar da muke yanzu, babu tallafin gwamnati a cikinta.
“Mun yi hakan ne ta hanyar kara kudin daga lokaci zuwa lokaci ba wai a lokaci guda ba,” inji Ministar.
Zainab ta kuma ce har yanzu tallafin mai ba karamar matsala ba ne ga gwamnati, inda ta yi gargadin cewa karuwar farashin man a kasuwannin duniya zai kara dagula al’amura.
A watan Oktoban 2021 ne dai Ministar ta sanar da cewa gwamnati ta tanadi biyan tallafin ne kawai a watanni shida na farkon 2022, a kokarinta na janye tallafin sannu a hankali.