Wasu matasa da suka kuduri aniyar bunkasa ayyuka da sana’o’insu a garin Malumfashi da kewaye, sun kafa kungiyar taimakon juna mai suna ABU Junction Youth Self-Help Co-operatibe Society, Malumfashi.
Shugaban kungiyar, Malam Abdulrahman Sani Total ya bayyana wa wakilinmu, cewa sun kafa kungiyar ce da nufin taimakon juna, musamman ganin yadda suke fuskantar kalubale daban-daban a sana’o’i da ayyukansu.
“Mun kafa kungiyarmu ne da nufin taimakon juna, musamman domin mu bunkasa sana’o’i da ayyukanmu. Haka kuma, za mu yi amfani da wannnan dama wajen jawo wasu daga cikin matasanmu da ba su da aiki ko sana’a, don mu agaza musu su samu aiki ko sana’a, ta yadda za su dogara da kansu. A fanni daya kuma, za mu yi amfani da kungiyar wajen tallafa wa al’ummar yankin Malumfashi da Jihar Katsina da ma kasa baki daya. Yana cikin kudurinmu, mu tallafa wajen tsabtace muhalli da gyaran makabartu da gyaran masallatai da da sauransu,” inji Abdulrahman, lokacin da yake jawabin gabatar da kungiyar, a wani kwarya-kwaryan taro da kungiyar ta gudanar a ranar Asabar da ta gabata a garin Malumfashi.
A ci gaba da jawabin, shugaban ya ce sun fara kungiyar ce da mutum biyar kacal, daga bisani suka koma mutum 15, a yayin da a yanzu haka sun kai mutum 30. “Mun sanya ka’idoji na musamman ga duk wanda zai shiga kungiyar nan, musamman domin mu kauce wa inna-rididi, domin Hausawa ma sun ce da haihuwar yuyuyu, gara da daya kwakkwara. Ke nan duk wanda zai shiga kungiyar nan sai ya cika fom, sannan ya dauki alkawarin zai nuna kishi da bin dokokin kungiya sau da kafa. Dalili ke nan ya sanya ba mu bude kofa kowa ya shigo ba, domin gudun kada bara-gurbi su bata mana tsarin da muka gina kungiyar a kansa,” inji shi.
kungiyar, wacce ta yi rajista da Gwamnatin Jihar Katsina, a ranar 3 ga watan Nuwamban bana, kuma ta mallaki lambar rajista, KTS 40492, tuni ta ci gaba da tafiyar da ayyukanta, inda ta tuntubi manya da iyayen da za su rika ba ta shawara da kuma tallafi wajen gudanar da ayyukanta.
A taron kungiyar da ya gudana a Asabar da ta wuce, bako mai jawabi, Bashir Yahuza Malumfashi, ya nuna farin ciki da matasan, kan yadda suka gane muhimmancin kungiya har suka kafa tasu, wacce kuma suka yi mata fandishan da tsari, ta yadda za su amfani da kawunansu da sauran al’umma.
Da yake ba su shawara domin dorewar muhimmin aikin nasu, Bashir ya bayyana musu cewa lallai ne su rike abubuwa hudu, a yayin gudanar da kungiyar. “Ina ba ku shawara ku lura kuma ku rike tare da sanya abubuwa hudu a zukatanku, a yayin tafiyar da wannan muhimmiyar kungiya. Na farko, ku sanya kalmar hadin kai a zukatanku, domin kuwa da hadin kai ne ake samun karfi da fa’idar bin manufofi da dokokinta. Na biyu, ku sanya gaskiya cikin lamurranku, domin duk abin da aka dora kan gaskiya, zai samu nasara, kuma muddin aka kauce mata, to komai dadewa al’amarin ba zai yi karko ko ya yi nasara ba. Na uku, ku sanya hakuri a dukkan lokaci. Hakuri shi ne babban tsanin da ke kai mutum ga nasara. A duk lokacin da mutum ya yi hakuri, to zai samu juriya, wadda ita kuma za ta sanya a aiwatar da abu komai wuyarsa. Duk abin da ka tsayu a kansa, ka aikata shi da hakuri da juriya, to komai dadewa sai ka ci gajiyarsa. Ba lallai ne a ce yanzu-yanzu za ka amfana da abin ba. Wani lokacin ma, ba kai da kanka ne za ka ci gajiyar aikin ba, sai na bayanka ne za su amfana, ko kuma ma ka tsinci ijararka a wurin Allah a Lahira. Abu na hudu da za ku nuna a yayin tafiyar da wannan kungiya mai albarka, shi ne ku kasance masu amana. Ku sani cewa duk taron da ya hadu, aka ce kuma babu rikon amanar juna, to tabbas babu inda al’amarin zai je. Don haka lallai ne ku san cewa wannan aiki da kuka dauka, amana ce a kanku, kuma amana ce ga al’ummar da kuke ciki. Allah sa mu dace amin.”
A yayain da yake karin bayani, Shugaban kungiyar ya bayyana cewa za su tafiyar da ayyukan kungiyarsu ba tare da nuna bambancin addini, kabilanci ko siyasa ba. Ya ce duk wanda zai kasance da shirin taimaka wa al’umma, to za su iya amsarsa a cikin kungiyar, kuma idan taimako ya zo, za su yi wa mutum ba tare da nuna bambanci ba. Haka kuma ya ce ba za su shiga harkar siyasa a kungiyance ba, domin kungiyarsu ba ta da alaka da kowace jam’iyyar siyasa. Ya ce za su fadada ayyukansu ta yadda kowa zai amfana, kamar kuma yadda ya dauki alwashin bayyana dukkan irin ayyukan da za su rika gudanarwa a kafafen watsa labarai da kuma kafofin sada zumunta na zamani, kamar Facebook da sauransu.
Saboda hadin kai da taimakon juna muka kafa kungiyarmu – Matasan Kwanar ABU Malumfashi
Wasu matasa da suka kuduri aniyar bunkasa ayyuka da sana’o’insu a garin Malumfashi da kewaye, sun kafa kungiyar taimakon juna mai suna ABU Junction Youth…