Ofishin Masarautar Saudiyya da ke Kula da Masallatan Harami na birnin Makkah da Madina, ya fitar da sabbin tsare-tsaren yadda za a gudanar da ibada a masallatan a cikin watan azumi na Ramadan.
Shugaban Ofishin kuma Babban Limamin Masallacin Harami na Makkah, Sheikh Abdulrahman Sudais ya gabatar da sabbin tsare-tsaren ga Yarima Mai Jiran Gado, Mohammed ibn Salman.
Bisa sabon tsarin, Saudiya ta cire mafi yawancin ka’idojin da ta sanya wa baki da masu zuwa Umrah daga ciki da wajen kasarta, gami da janye yawancin matakan dakile yaduwar cutar COVID-19 a kasar.
Sabbin tsare-tsaren da Saudiyya ta fitar:
A yanzu babu sharadin allurar rigakafin COVID-19, saboda haka mutanen da ba a yi wa allurar ba na iya zuwa Umrah.
Haka kuma babu bukatar gabatar da shaidar karbar allurar rigakafin cutar idan aka isa kasar.
An soke bayar da tazara a Masallatan Harami biyu
Babu kayyade yawan mutanen da za su shiga Masallatan domin yin sallah ko Umrah.
Babu bukatar samun izinin shiga masallatan domin sallah, Umrah ko ziyara.
An soke lokacin da aka kayyade na jira kafin samun takardar bizar zuwa Umrah. Yanzu duk wanda ya nema zai samu, gwargwadon lokacin da ya nema.
Babu kayyade yawan mutanen da za su yi Umrah a watan Ramadan.
An soke dokra hana yin bude baki a taron jama’a.
Za a dawo da shimfidun bude bakin gandu.
Masallatan Harami za su kasance a bude cikin duk sa’a 24 ta kowacce rana.
Za a ci gaba da Itikafi daga ranar 20 ga watan Ramadan har zuwa daren ranar Karamar Sallah.