Kawo yanzu mutum 15 ne suka daga jam’iyyu daban-daban suka lashe zabe domin zama gwamna a karon farko a jihohin Najeriya.
Takwas daga cikin sabbin gwamnonin sun ci zaben ne a karkashin inuwar Jam’iyyar APC, 1 a NNPP sai wasa bakwai a babbar jam’iyyar adaawa ta PDP.
Ga jerin sunayen sabbin gwamnonnin:
Sabbin gwamnoni daga APC
- Ahmad Aliyu — SAKKWATO
- Bassey Otu — KUROS RIBA
- Dikko Umar Radda — KATSINA
- Francis Nwifuru — EBONYI
- Hyacinth Alia — BINUWAI
- Uba Sani — KADUNA
- Umaru Bago — NEJA
- Umar Namadi — JIGAWA
Sabon gwamna daga NNPP
- Abba Kabir Yusuf (NNPP) — KANO
Sabbinoni daga PDP
- Caleb Mutfwang (PDP) — FILATO
- Dauda Lawal Dare (PDP) — ZAMFARA
- Kefas Agbu (PDP) — TARABA
- Sheriff Oborevwori (PDP) — DELTA
- Siminialayi Fubara (PDP) — RIBAS.
- Umo Eno (PDP) — AKWA IBOM.
A ranar 18 ga watan Maris da muke cikin ne Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta gudanar da zaben gwamnoni a jihohi 28 da ke kasar mai yawan jihohi 36 da kuma babban birnin Tarayya.
Sauran johohi takwa da ba a gudanar da zaben ba, nasu zaben gwamnonin na gudana ne a lokuta daban-daban, saboda wasu dalilan da suka sa zaben nasu ya bambanta.
A birnin tarayya dai ba a gwamna.