Wasu mata sun samu kansu a cikin damuwa bayan da sababbin ’yan hayar gidansu suka tsere da ’ya’yansu hudu, kwana uku da kama haya a gidan da suke a Umu’ahiya fadar Jihar Abiya.
’Yan hayar da aka sace wa ’ya’yan, Ngozi Kingsley da Madam Ifeyanyi Uduma ’yar uwar Ngozi Kingsley da Blessing Peter Obasi daga gidan Nwoke da ke Enugwu, Nguzu Edda a Jihar Ebonyi dukkansu suna kasuwanci ne a Umu’ahiya.
Su bayyana cewa sababbin ’yan hayar mata su biyu wadanda ba su rike cikakken sunayensu ba, sun tare a gidan da suke haya ne a ranar Alhamis 15 ga Disamban nan a dakin da suka karba haya da ’yar katifarsu da karamin abin girki na gas da kuma babbar jakar Ghanamust-go guda daya.
Sun ce cikin sakin fuska farin ciki da walwala suka ja kowa a jika musamman yaran gidan inda suke ba su abubuwan kwalam da makulashe har da abinci wanda hakan ya sa kowa ya saki jiki da su har yaran suke shiga dakin matan suna wasa a cikin kwana biyu da tarewarsu.
- Zargin N1.2bn: Emefiele ya fito daga gidan yari
- Yadda Aka Fara Gasar Alkur’ani ta Kasa Karo Na 38 A Yobe
A rana ta uku sai bakin matan suka shammaci iyayen yaran inda daya daga cikin bakin matan dauke da babbar jaka cike da kaya ta ce za je unguwa wuri ’yar uwarta ta kai kayan, ta kuma fita a idon daya daga cikin iyayen yaran mai suna Uduma, yayin da daya abokiyar hayarta ke zaune da sauran gidan suna ta wasansu.
Bayan ta tafi sai daya bakuwar ’yar hayar ta ce bari ta je da sauran yaran su sayo biskit a shago sai suka fita, fitar da ba su dawo ba har dare, hakan ya sa aka shiga nemansu da lamarin ya ci tura aka je babban ofishin ’yan sanda aka sanar da su da kuma neman dauki.
Kakakin ’Yan sandan Jihar, Maureen Chinaka wadda ta tabbatar da labarin ta ce, “Yanzu haka sun kama wasu da suke da alaka da sababbin ’yan hayar, kuma an fara bincike don gano inda yaran suke.”