✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sababbin shugabannin MOPPAN ta Katsina sun saba laya

An rantsar da sababbin shugabanin Gamayyar kungiyoyin Masu Shirya Fina-Finan Hausa wato Motion Pictures Practitioners Association of Nigeria MOPPAN) reshen Jihar Katsina a ranar Asabar…

An rantsar da sababbin shugabanin Gamayyar kungiyoyin Masu Shirya Fina-Finan Hausa wato Motion Pictures Practitioners Association of Nigeria MOPPAN) reshen Jihar Katsina a ranar Asabar da ta gabata. 

Bikin rantsarwar wanda ya samu halatar Shugaban kungiyar MOPPAN ta kasa Alhaji Abdullahi Maikano an yi shi a dakin taro na Katsina Motel. 

Shugabar kungiyar Hilwa ta Jihar Katsina Hajiya Mariya Abdullahi wadda ta bayyana goyon bayansu ga wannan kungiya, ta ce, “Mace ce abokiyar ci gaban rayuwa idan muka yi la’akari tun daga farkon halittar mutum, wato kakanmu Annabi Adamu wanda aka halitta masa mace domin su ci gaba da rayuwa.”

Shi kuwa Sa’in Katsina Alhaji Amadu Na Funtuwa, cewa ya yi masu wannan harka ta shirya fina-finai su ne kan gaba a wannan lokacin wajen fadakar da al’umma saboda haka nauyi ne a gare su da ya zama wajibi su sauke. 

Shugaban kungiyar ta kasa Alhaji Abdullahi Maikano kara nanata musu dokokin kungiyar ya yi tare da kara ja musu hankali a kan rike sana’ar da kuma kare mutuncinta. 

Sabon Shugaban kungiyar Kwamared Lawal Rabe Lemu ya ce zai yi iya kokarinsa don ganin ya sake hada kan ’ya’yan kungiyar ta jihar. Sannan ya ce, “An Allah Ya so za mu yi kokarin maido da martabar jihar nan wadda ita ce tushen hada kan masu wannan sana’a. Kuma za mu yi kokarin ganin cewa fina-finan da za mu ci gaba da yi sun nuna al’adunmu na Hausawa. Sannan za mu bi dokar kungiya a wajen batun hulda a tsakanin maza da mata a yayin daukar fim. Sannan ina kira ga jama’a su shigo cikin wannan sana’a ta hanyar saka jarinsu.”

Sababbin shugabannin sun yi rantsuwar kama aiki ne a hannun Barista Dikko Abbas. Shugabannin sun hada da Kwamared Lawal Rabe Lemu a matsayin shugaba sai Aminu Musa Bukar Mataimakin Shugaba. Sai Hamisu Lawal Sakatare sai Aminu Dagash Mataimakin Sakataren sai Abubakar Ayuba Masanawa Ma’aji. Sai Hauwa’u Suleiman Sakatariyar Kudi da Ibrahim Sani ya Mai Binciken Kudi. Rabe Halliru kuma Sakataren Tsare-tsare. Rabi’u M. Yaro da Fatima Ladan suna rike da mukamin jami’an hulda da jama’a na daya da na biyu.