✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sa’a Ibrahim: Kallabi tsakanin rawuna

Hajiya Sa'a Ibrahim ta kafa tarihi wajen kasancewa ta farko a bangarori da dama

Hajiya Sa’a Ibrahim ce mace ta farko ta kai wasu matakai a harkar yada labarai ba kawai a Jihar Kano ba, har ma a Najeriya.

Ko kafin ta zama mace ta farko da ta hau kujerar Manajan Darakta kuma Darakta Janar ta gidan talabiji na Abubakar Rimi (ARTV) a 2014, ita ce mace ta farko da ta zama shugabar wani sashe a gidan Rediyo Kano.

Sannan kuma yanzu haka ita ce Shugabar Kungiyar Gidajen Rediyo da Talabijin na Najeriya (BON) – mace ta farko da rike wannan mukamin a shekara 32.

Ko a ARTV din ma kuma, Hajiya Sa’a ta kafa tarihi bayan da ta mayar da shirye-shiryen tashar sa’o’i 24.

Shekara fiye da 30 a aikin jarida

Ta yi digirinta na farko ne dai a fannin Kimiyyar Siyasa, sannan ta yi digiri na biyu a fannin Hulda da Jama’a, duk a Jami’ar Bayero ta Kano.

Bayan nan kuma Hajiya Sa’a Ibrahim ta yi karatun difloma a fannin Shirye-Shiryen Rediyo a Jami’ar Jos.

Bayan aikin da ta yi da kafofin yada labarai, ta kuma yi da hukumomi na gida da na waje don wayar da kan al’umma a kan al’amura da dama.

Alal misali, ta yi aiki da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) wajen tsarawa da aiwatar da shirye-shiryen bayar da allurar riga-kafin kamuwa da polio da kuma Shirin magance tamowa a Jihar Kano.

Bugu da kari, Tauraruwar ta taimaka wajen tsara shirye-shiryen wayar da kai game da muhimmancin shayar da nonon uwa da hanyoyin rage mace-macen mata yayin haihuwa da sauransu.