Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce sama da ’yan bindiga 50 ne suka mutu bayan da jiragen yaki suka yi musu ruwan wuta a Jihar.
An dai kai hare-haren ne yankin Saulawa da Farin Wata da ke Karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar.
- Allah ya yi wa babbar jikar Sardauna rasuwa
- Mutumin da ke kai wa ’yan bindiga abinci da fetur ya shiga hannu a Kano
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Mista Samuel Aruwan ne ya fitar da sanarwar a ranar Talata.
A cewarsa, jiragen yakin rundunar sojin Najeriya ne suka yi wa ’yan bindigar da suka addabi yankin Dogon Dawa zuwa Damari zuwa Saulawa barin wuta.
Ya ce bayan sintiri da jirgin yakin farko ya yi, an gano wasu ’yan bindiga su biyar a kan babura kilomita hudu da garin Saulawa, suna dakon bude wa jirgin wuta.
“An musu barin wuta ta ko ina, an hango ’yan bindiga kimamin su 50 a kan babura suna tserewa kuma nan take aka bude musu wuta,” a cewar Aruwan.
Kwamushinan ya ce daga bisani kuma an sake tura wani jirgin yaki, wanda ya taimaka wajen kashe maharan yayin da suke kokarin tserewa.
Bincike ya tabbatar da cewar an kashe sama da ’yan bindiga 50 ne a yayin ruwan wutar da jiragen suka yi a yankin na Birnin Gwari.