✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ruwa ya halaka zakaran damben Legas

Shugabanni da ’yan wasan damben zamani na Jihar Legas sun ga tashin hankali yayin da zakaran damben jihar a rukunin masu matsakaicin nauyi, mai suna…

Shugabanni da ’yan wasan damben zamani na Jihar Legas sun ga tashin hankali yayin da zakaran damben jihar a rukunin masu matsakaicin nauyi, mai suna Philip Eugene Hope ya mutu yayin da yake wanka a cikin ruwan da ke cibiyar wasanni ta Mobolaji Johnson da ke filin shakatawar da ake kira Rowe Park na unguwar Yaba a Legas.
Aminiya ta gano cewa Eugene Hope wanda shi ne zakara a gasar wasan damben da hukumar wasanni ta jihar ta shirya a bana na masu matsakaicin nauyi ya gamu da ajalinsa ne yayin da ya je kallon wasan damben abokanen hamayyarsa da aka yi a filin shakatawa na Rowe Park a jihar a karshen makon da ya gabata.
Wadanda lamarin ya auku a kan idonsu sun bayyana cewa yana shiga harabar filin shakatawar sai ya yanke shawarar ya nufi wurin ruwa domin ya shiga ya yi wanka kafin a fara wasa.
daya daga cikin ma’aikatan wurin mai suna Idowu Ephanus ya ce ‘Da farko mun hana shi shiga muka ce sai ya biya amma da ya nuna mana cewa shi ne zakaran damben Legas kuma muka gamsu da haka sai muka kyale shi, nan da nan ya tube kayansa ya fada cikin ruwan, jim kadan da fadawarsa sai ya nutse ba mu ankara ba, can da muka ga bai dago ba sai muka shiga domin mu ceto shi. Kafin mu kai gare shi ya riga ya sha ruwa da yawa, da muka fito da shi sai muka ga ruwa yana fita ta hancinsa da bakinsa da idanunsa, sai aka yi kokarin kai shi asibiti inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa’.
Shugaban wasan dambe na jihar Legas, Alhaji Monsuru Liasu ya ce ‘Wannan lamari abin bakin ciki ne, Philip ya tafi. Yaro ne da ya zama zakaran damben a kwanannan, gaskiya mun yi bakain ciki’.
Mutane da dama sun bayyana Philip a matsayin dan wasan dambe mai hazaka da kwarewa wanda yake da bajintar iya naushi.