✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ruwa ya ci ’yan mata hudu a Jigawa

Sun nutse a kogi a lokacin da suke kokarin ketarawa su tafi gona a yankin Gwaram, Jihar Jigawa

’Yan sanda a jihar Jigawa sun tsamo gawarwakin wasu ’yan mata hudu da suka nitse a ruwa a Karamar Hukumar Gwaram ta Jihar.

Rahotanni sun nuna cewa ’yan matan sun nitse a kogin ne lokacin da suke kokarin tsallaka shi domin zuwa gona.

A ranar Talata Kakakin Rundunar ’Yan Sanda a jihar, ASP Abdu Jinjiri shine ya tabbatar da aukuwar lamarin wanda ya ce ya faru ne da misalin karfe 10 na safiyar ranar a kauyen Sara na karamar hukumar ta Gwaram.

Ya ce wadanda iftila’in ya rutsa da su sun hada da Bilkisu Haruna mai kimanin shekara 17; Shamsiyya Nuhu mai shekara 13; da Maryam Danlami mai shekaru 12; dukkansu daga kauyen Kafin Doka Yamma.

Sai dai ya ce har yanzu ana ci gaba da neman gawar wata yarinyar mai suna Marakisiyya Musa mai shekara 12 wacce ba a kai ga gano ta ba.