Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce rushe sashen ’yan Sanda na FSARS mai yaki da fashi shi ne matakin farko na gyaran fuska ga aikin dan sanda a Najeriya.
Buhari ya kuma ba da umarnin a hukunnan dukkannin jami’an sashen da suka aikata laifukan da suka saba ka’idojin aiki.
A jawabinsa ga taron shirin aikin tallafin gwamnati ga matasa 774,000 a ranar Litinin, Buhari ya ce,
“Zan yi amfani da wannan dama in yi tsokaci kan sahihan korafe-korafen ’yan Najeriya game da amfani da karfe fiye da kima, kisa ba bisa ka’ida ba, da kuma saba doar raiki da ’yan sanda ke yi.
“Rushe SARS matakin farko ne a shirinmu na yin cikakken kwaskwarima don ganin babban aikin ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro shi ne kare rayuka da dukiyoyoin jama’a.
“Za kuma mu tabbatar da an hukunta dukkannin wadanda ke da hannu a laifukan da suka aikata.
“Muna matukar takaicin asarar ran matashi da aka yi a Jihar Oyo a lokacin zanga-zangar kwanan nan.
“Na kuma ba da umarnin a gudanar a cikakken bincike kan musabbabinsa.
“Duk da haka yana da muhimmanci a lura cewa akwai ’yan sanda maza da mata masu da yawa masu jajircewa wajen yin aikinsu tukuru.
“Kar a bari ’yan tsirarun baragrubin cikinsu su zubar da kimar rundunar”.
A ranar Lahadi, Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Muhammad Adamu, ya soke SARS bayan jerin zanga-zangar da aka gudanar a wasu manyan biranen Najeriya na zargin jami’an sashen da cin zarafi, a wasu lokuta ma har da kisa, zargin da rundunar ta musanta.
A wajen zanga-zangar ne harsashin ’yan sandan kwantar da tarzoma ya kashe wani matashi mai suna Isaq Jimoh tare da jikata mutum uku da a yanzu suke kwance a asibiti.
Buhari ya yi bayanjin ne a jawabinsa ga taron kaddamar da shirin samar wa matasa 774,000 ayyukan yi na P-YES, a ranar Litinin.
A nasa bangaren mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbanjo cewa ya yi, amfanin jami’an tsaro shi ne, su tabbatar da kariya ga rai da rayuwar al’umma.
Taron ya kuma samu halarcin Shugabancin Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan da Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano da kuma takwaransa na Jihar Ebonyi, Injiniya Dave Umahi.