Kungiyar dattawan jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Gombe ta yi Allah-wadai da yadda ta zargi gwamnatin jihar da rusa ofishin yakin neman zaben dan takarar gwamnanta, Muhammad Jibrin Dan Barde.
Shugaban kungiyar, Alhaji Bala Muhammad Magaji, ne ya bayyana hakan a madadin dattawan a taron manema labarai da suka kira ranar Alhamis a Gombe.
- Yadda ambaliya ta rusa gidan mutumin da ke rubutu da kafa
- Sannu a hankali Najeriya na komawa mulkin kama-karya – Jonathan
Sun bayyana rusa musu ofishin a matsayin siyasa da kuma neman tayar da zaune tsaye.
Ya ce, “A watannin baya, gwamnati ta rusa ofishin, yanzu ta sake rusawa me take nufi da hakan, kowa na da ’yancin yin siyasar da yake so, dan me za a dinga rusa musu ofishin yakin neman zaben dan takararmu?”
A cewar sa, Gwamnan ya ce ofishin yana kan hanyar unguwar GRA ne sannan kuma ya yi kusa da Gidan Gwamnati ne ya sa aka rusa shi, wanda AlhajiMuhammad ya ce hakan ba uzuri ba ne.
“[Gwamna] Inuwa ka manta a lokacin da PDP ke mulki a shekarar 2018, ka yi amfani da wajen a matsayin ofishin yakin neman zabenka bayan da Dan Barde ya fadi a zaben fid-da gwani ya baka wajen ka mayar da shi na yakin neman zabenka kana APC sai yanzu ne da ka zama Gwamna za ka ce ya yi kusa da gidan gwamnati?,” inji dattawan.
Sun yi kira ga Gwamna Inuwa Yahaya cewa ya sani fa gwamnati ta al’umma ce kuma sun zabe shi ne dan kare rayuka da dukiyoyinsu, ba dan rusa kadarorinsu ba.
Rusa ofishin ba shi da alaka da siyasa – APC
A bangaren jam’iyya mai mulki ta APC a jihar, ta bakin kakakinta na jihar, Moses Kyari, cewa ya yi wannan ofis da aka rusa ba na Dan Barde ba ne na wata kungiya ce mai rajin samar da shugabanci nagari (Gombe good leadership Initiatives) wadda dan takaran gwamna na jam’iyyar PDP ke amfani da shi a matsayin ofishin yakin neman zabe.
Kyari ya ce yamadidin siyasa da ake yi kan lamarin abin takaici ne, ganin yadda ’yan adawa ke siyasantar da batun, lamarin da kwata-kwata ba shi da nasaba da siyasa”.
Ya ce kungiyar ta rubuta wa Hukumar Raya Birane ta Jihar Gombe (GOSUPDA) bukatar neman izinin wucin-gadi da sanya allunan tallan ’yan takara, kuma hukumar ta amince mata.
“Amma a lokacin da hukumar ta fita aikin sanya ido da takan yi a jihar, sai ta gano cewa kungiyar har ta fara yin gini na din-din-din maimakon damar wucin-gadi da aka bata, hakan yasa ta tura wa kungiyar wasikun gargadi cewa ta dakatar da ginin”.
Ginin ofishin ya saba wa ka’ida – GOSUPDA
Ita ma hukumar ta GOSUPDA ta ce ta rusa ofishin kungiyar samar da jagoranci nagari ta Gombe, wanda dan takaran yake amfani da shi a matsayin ofishin yakin neman zabe ne saboda ofishin ya saba wa ka’ida da dokokin hukumar.
Ta kuma ce ofishin zai haifar da barazanar tsaro a yankin.
Shugaban Hukumar ta GOSUPDA, Guruf Kyaftin Peter Bilal (mai ritaya) ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai, jim kadan bayan sanya ido kan aikin rushe ginin.
Ya ce, “Kungiyar samar da jagoranci nagari ta Gombe ta mayar da ofishinta zuwa na yakin neman zabe ne na din-din-din na dan takarar gwamnan PDP, alhali kuwa izinin wucin-gadi suka nema, muka ba su.”
Kyaftin Bilal ya ce a yayin da hukumar take gudanar da ayyukanta kamar yadda doka ta tanadar a sashe na 27 na dokar raya birane ta Jihar Gombe na shekarar 2011, ta ba wa ofishin wasikar dakatar da aiki tare da rushe wurin.