Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna ta fara bincike kan shanu 30 da awaki uku da suka yi batan dabo a hannunta.
Babban Jami’in ’Yan sanda mai kula da birnin Kaduna, (Metro), Surajo Fana ne ya tabbatar wa da mai shanun, Ibrahim Abdullahi haka lokacin wata ganawa da suka yi a ofishinsa a Kaduna a ranar Litinin.
An yi ganawar ce da misalin karfe 3:30 na rana a ofishin Metro da ke Panteka, Kaduna, kuma an yi ganawar ce a kan idon tsohuwar Kwamishinar Mata ta Jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Baba.
A lokacin ganawar an dauki bayanan dattijon dangane da zargin bacewar shanunsa a hannun ’yan sanda.
Babban jami’in ya tabbatar wa da dattijon da ita Hajiya Hafsat Baba cewa an umarce shi ne ya kira su wannan taro ne domin a fara binciken ainihin yadda aka yi shanun suka bace.
Ya tabbatar musu da cewa zai yi adalci a kan wannan aiki da aka ba shi ba tare da ya nuna son kai ba.
Da take bayani ga Aminiya bayan sun fito daga taron, Hajiya Hafsat Baba ta ce a shirye take ta bai wa ’yan sandan duk wani taimako da suka bukata da zai taimaka wajen gano gaskiyar inda shanun suke.
“Eh, an gayyace mu ni da shi mai shanun zuwa ofishin ’yan sanda na Metro domin a tattauna. Jami’in ’yan sandan ya shaida mana cewa an umarce shi ya gudanar da bincike a kan bacewar wadannan shanu kuma ya ba mu tabbacin cewa zai yi adalci. Ya kuma ce duk wanda aka samu da laifi komai mukaminsa ba za a kyale shi ba. Don haka muka nuna masa cewa a shirye muke mu ba shi duk goyon bayan da yake bukata domin a yi adalci ga wanda aka zalunta,” inji ta.
Ta ce za ta ci gaba da bibiyar wannan zance har zuwa lokacin da za a gano masu hannu wajen bacewar shanun.
A wata sabuwa kuma, binciken da wakilinmu ya yi ya gano cewa wata kotu a Jihar Kaduna ta bai wa rundunar ’yan sanda umarnin ta mayar wa wadannan Fulani shanunsu da ta kwace.
Takardar umarnin wanda wakilinmu ya samu na dauke ne da sa hannun alkalin kotun Abdul’azeez Ibrahim. Ya kuma saka hannunsa a takardar ce tun a watan Agustan bara.
Amma kimanin wata tara da aika wa ’yan sandan wannan umarni na kotu har yanzu babu wanda ya san inda shanun suke kuma ba a mai da wa masu shanun su ba.