✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta karrama Sheikh Abdulwahab Abdullah

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta karrama babban Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Abdulwahab Abdallah da lambar yabo kan zaman lafiya. Rundunar ’yan sandan a Yammacin…

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta karrama babban Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Abdulwahab Abdallah da lambar yabo kan zaman lafiya.

Rundunar ’yan sandan a Yammacin ranar Talata 22, ga watan Disambar 2020, ta karrama Shehin Malamin karkashin jagorancin Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kano, CP Habu A Sani.

Kwamishinan ya ce, sun karrama Malamin ne bisa kokarinsa wajen kwantar da hankalin jama’a da kwadaitar da mutane kan muhimmancin zaman lafiya a Jihar Kano da ma kasa baki daya.

Sheikh Abdulwahab Abdullah, Malami ne da ya shahara wajen karantarwa da sulhunta tsakanin ma’aurata da fadakar da al’umma kan muhimmancin zaman lafiya a karantarwarsa a Jihar Kano da kasa baki daya.

 

%d bloggers like this: