Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta haramta al’adar nan ta Tashe da aka saba gudanarwa da zarar watan azumi na Ramadana ya kai kwanaki goma.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Litinin.
- Harin Filato: An gano gawawwaki 50, gidaje fiye da 100 sun kone
- Ministar Harkokin Wajen Jamus na ziyarar aiki a Yammacin Afirka
“Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano karkashin jagorancin Kwamishina CP Sama’ila Sha’aibu Dikko na sanar da al’ummar Jihar Kano cewa, a dakata da gudanar da al’adar nan ta Tashe, wadda ake yin ta daga 10 ga wata Azumin Ramadana.
“Wannan ya biyo bayan fakewa da wasu bata garin matasa ke yi da tashen suna fadan daba, kwacen waya da kuma ta’ammali da miyagun kwayoyi.
“Sanarwar tana kuma taya daukacin al’ummar musulmi murna da fatan azumin ya zama karbabbe a wurin Allah.”
SP Kiyawa ya yi kira ga iyaye da su tabbatar sun gargadi ’ya’yansu a kan karya wannan dokar, domin kuwa babu shakka doka za tayi aiki akan duk wanda ya saba.
Bisa al’ada, idan azumin watan Ramadan ya kai kwanaki 10, akwai al’adar Tashe da kuma kidan gwauro da ake gudanarwa a kasar Hausa.