Tashe wata al’ada ce da ake gudanarwa daga kwana 10 na watan Ramadan har zuwa daren sallah.
Masu tashe, yawancinsu kananan yara, cikin shiga ta ban dariya, sukan zaga kwararo-kwararo a unguwanni da kasuwanni suna nishadantar da mutane da abubuwan barkwanci da ba’a da dai sauransu domin debe musu gajiyar azumi.
A yayin da aka shiga lokacin gudanar da tashe, ’yan sanda sun takaita yin sa saboda wasu dalilai.
Aminiya ta binciko muku asali da tarihi da sauran muhimman abubuwa game da wannan al’ada da ke gudana a cikin watan Ramadan mai alfarma, a kasar Hausa.
Asalin kalmar tashe
Masana sun bayyana cewa asalin tashe ana yin sa ne da dare, kuma bakuwar al’ada ce da malam Bahaushe ya samu daga baya.
Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza malami ne a Sashen Koyar da Harsunan Najeriya a Jami’ar Usmanu Danfodio da ke Sakkwato.
Ya bayaya wa Aminiya cewa, “Kalmar tashe ta samo asali ne daga a tashi, wato a tashe su daga barci.”
Tarihin tashe
Ita dai wannan al’ada a cewar Farfesa Bunza, ba a san bahaushe da ita ba sai bayan zuwan Musulunci kasar Hausa.
Tashe “Ya samu tarihin Bahaushe ne a watan azumi na Ramdan; wannan ya nuna bakon abu ne, domin gabanin zuwan Musulunci babu,” inji shi.
Ya ce masana al’ada na ganin tashe ya samo asali ne daga Daular Andalus, “Can ne Musulmi suka kusa kusanta da al’adu, domin da kidin taushi da tashe duk daga can suka samo asali.”
Dalilin yin tashe
Farfesa Bunza ya bayyana cewa asalin makasudin yin tashe shi ne a tayar da mutane daga barci su yi sahur a watan azumin Ramadan.
“Har yanzu [a Daular Andalus] suna yin tashen, wanda za a tayar da mutane da dare domin su samu su yi sahur.”
Daga baya “Abin ya koma wasan yara na jan hankalin jama’a da faranta musu rai da debe musu gajiya da takaici da wahala.”
Tashe a al’adar Bahaushe
A kasar Hausa akan fara yin tashe ne a 10 na tilas, wato kwana 10 na biyu cikin watan Ramadan domin sanya wa mutane nishadi.
Bahaushe ya kasa watan azumin Ramadan zuwa gida kuna: 10 Na Marmari, 10 Na Wuya, da kuma 10 Na Dokin Sallah.
Malamin ya bayyana cewa Bahaushe ya zabi 10 Na Wuya a matsayin lokacin fara tashe.
“10 Na Marmari Bahaushe ya ga bai ma kamata a yi tashe a lokacin ba, sai an shiga 10 Na Wuya, lokacin an dan fara gajiya da azumin.
“Saboda haka sai a riƙa yin tashe ana sa mutane fara’a da farin ciki, su kuma suna ba da kyauta da sadaka.”
Muhimmancin Tashe
Game da hikima da kuma amfaninsa, Farfes Bunza ya ce tashe kan nuna duk yanayi da mutane suke ciki a shekarar, kuma akwai darasi a cikinsa.
“Su yaran suna kokarin su bayyana halayya da duk wani yanayi da mutane suke ciki.
“Da za a saurari tashen yaran za a ga manyan maganganu ne da manya suka sa musu a baki.
Ya ce, “Cikin tashe ana gina wa yara kunya, kokari, kwazo, son gaskiya, son juna da sauransu.”
Tasirin tashe
“Malamai sun gaya mana cewa tashe shi ne musabbabin samuwar wasu fitattun mawakan kasar Hausa; daga wakokin tashe suka samu shahara, maza da mata.
“Saboda haka tashe wani abu ne na sada zumunci da kokarin lurar da mutane [irin] halin da ake ciki, da yadda ya kamata a fuskance su.
“Don yanzu ga shi nan na ga wata yarinya tana tashe a kan bilicin, ba mamaki a samu wata kuma tana tashe a kana ta’addanci.
“Mu nuna wa mutane cewa ta’addanci fa ba zai yiwu ba, dole mu zauna lafiya; saboda haka yaran nan karatu ne suke mana mai zurfi.”
Bana babu tashe a Kano
Sarkin Gwagwaren Kano, Auwalu Sani Nalako ya tabbatar wa Aminiya cewa bana babu wasan tashe da aka saba yi daga 10 ga watan Azumi duk shekara.
A tattaunawarsa da Aminiya, Nalako ya ce dalilin tsaro da Rundunar ‘Yan Sandan Jihar ta bayar ne ya sanya su ma suka dakatar da wasannin tashen na bana.
Sai da ya ce al’ummar yankunan jihar daban-daban za su iya yi a cikin unguwanninsu.
Dangane da wasan tashen gidan Sarkin Kano da suka saba yi kuwa, ya ce suna dakon dawowarsa daga tafiyar da ya yi ne domin jin ta bakinsa kan yiwuwar hakan.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da aka taba hana tashe ba a jihar a dalilin tsaro.
Domin ko a shekarar da ta gabata wasu wuraren sun hana yin tashen, musamman unguwannin da ke tsakiyar birnin Kano, saboda yadda wasan a shekarun bayan-bayan nan yake rikidewa zuwa rikici.
Bisa al’ada dai ana yin wasannin tashe ga wanda ya yi aure amma ya mutu, da gidajen masu kuɗi, sarakuna, da sauransu.