✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rundunar sojin sama za ta dauki sabbin hafsoshi aiki

Za a bude shafin har na tsawon kwanaki 35.

Rundunar sojin sama ta Najeriya NAF, ta sanar da bude shafin intanet na daukar sabbin sojoji a matakin hafsoshi wato Direct Short Sevice.

Wani babban jami’in rundunar, Air Vice Marshall Mahmud Mahdi ne ya sanar da hakan a madadin Babban Hafsan Sojan Ruwa na Kasa.

Sanarwar ta ce duk dan asalin Najeriya mace ko namiji mai sha’war aikin na da damar neman gurbin matukar ya cika dukkan sharudan da ta gindaya.

Rundunar ta ce za ta bude shafin daga ranar 26 ga watan Yuli sannan ta rufe shi a ranar 30 ga watan Agusta, 2021.

A cikin shafin ne mai sha’awar samun aikin zai ga dukkan sharuda da ka’idodin da rundunar take bukata.

Kadan daga cikin ka’idodin sun kayyade cewa masu neman aikin su kasance sun mallaki shaidar kammala digiri da babbar daraja ta biyu wato Second Class Upper.

Sannan ta nemi masu neman su kasance sun mallaki shaidar bautar kasa doriya a kan shaidar kasancewarsu ’yan kasa kuma wadanda basu yi aure ba.

Ta jaddada cewa shigar da bayanan masu neman aikin kyauta ne saboda haka su ankara da mazambata.

%d bloggers like this: