Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta sanya wa sabon dakin matuka jirgin saman Sashen Syyuka na Musamman na Runduna ta 115 da ke Fatakwal, Jihar Ribas, sunan matukiyar jirgin yaki mace ta farko a Najeriya, marigayiya Tolulope Arotile.
A yayin kaddamar da ginin a ranar Talata, Babban Hafsan Sojin Sama na Najeriya, Air Mashal Sadique Abubakar, ya ce sadaukarwar ta zama wajibi domin jinjina wa yadda Tolulope da sadaukar da rayuwarta tare kuma da karfafa gwiwar wadanda ke aikin yanzu cewa ba za a manta da su ba ko bayan ba su.
“Ina matukar farin ciki yau kasancewar mun taru ne a nan domin kaddamar da daya daga cikin ayyukanmu, wato dakin matuka jiragen saman Rundunar Ayyuka na Musamman ta 115 da ke Fatakwal wanda muka sanya wa sunan Tolulope Arotile, mace ta farko mai tuka jirgin saman yaki a Najeriya, wacce ta rasu ranar 24 ga watan Yulin, 2020 tana da shekaru 24”, inji Babban Hafsan.
Ya kara da cewa matakin ya zo daidai da kokarin karrama dukkannin wadanda suka yi fice wajen sadaukar da kai ga kasarsu ta hanyar tabbatar da cewa ba a manta da su ba.
“Muna fatan wannan yunkurin ba wai kawai zai taimaka wajen tunawa da ita ba ne kawai; muna sa ran zai taka rawa wajen kara wa yara mata gwiwar mayar da hankali a harkar karatu da yin aiki tukuru har su cimma burinsu a rayuwa su kuma bauta wa kasarsu cikin alfahari da sadaukarwa”, inji shi.
Daga nan sai babban hafsan ya yi kira ga mata da su yi koyi da marigayiya Tolulope wajen shiga rundunar, yana mai cewa ba su day wani shamaki kan nasarorin da za su iya samu a ciki.