✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rugunstumin rantsar da Buhari da gwamnoni: Buhari ya sava laya a karo na biyu

A shekaranjiya Laraba ne aka yi bikin sake rantsar da Shugaban Qasa Muhammadu Buhari a karo na biyu da Gwamnoni a Jihohi 29 da ke…

A shekaranjiya Laraba ne aka yi bikin sake rantsar da Shugaban Qasa Muhammadu Buhari a karo na biyu da Gwamnoni a Jihohi 29 da ke faxin qasar nan.

An yi bikin rantsar da shugaba Muhammadu Buhari ne a filin Eagle Suqare da ke Abuja.

Da misalin qarfe 8 da rabi na safe jama’a suka riqa tururwa musamman manyan baqi don halartar bikin rantsarwar.  Sai dai rahotanni sun nuna da yawa daga cikin tsofaffin shugabannin Najeriya ba su halarci bikin rantsuwar ba.  Tsofaffin shugabannin qasa irin su Cif Olusegun Obasanjo da Goodluck Ebele Jonathan da Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Janar Abdulsalami Abubakar ba su halarci bikin ba.  Amma rahotanni sun ce Abdulsalami Abubakar ba ya qasar ne a lokacin da aka yi bikin.  Amma Janar Yakubu Gowon da Cif Ernest Shonekan sun halarci bikin rantsarwar a matsayinsu na tsofaffin shugabannin qasa.

A wajen bikin, xaukacin tsofaffin Ministocin da suka yi aiki tare da Buhari a zangon farko sun halarta amma Ministan ayyukan gona da raya karkara Cif Audu Ogbeh ne kaxai ya halarci wajen bikin da motar gwamnati ta ba shi don gudanar da aiki duk da wa’adin mulkinsa na Minista ya qare.

Jim kaxan bayan an rantsar da shugaba Buhari sai ya nuna cewa a wannan karon zai zage damtse wajen ganin ya ba maraxa kunya.  Sannan a wata hira da aka yi da shi ana gab da rantsar da shi ya ce “zai ba maraxa kunya a wannan karo”.  Hasalima duk masu yi masa kirari da ‘Baba Mai Tafiyar Hawainiya’  a wannan karon za su sha mamaki, don zai tabbatar ya daidaita al’amurran ta hanyar yin mulkin da babu sani, babu sabo.

Haka kuma rahotanni sun ce jim kaxan bayan an rantsar da shugaban qasar ne sai yaq wuce Saudiyya a jiya Alhamis.  A wata hira da aka yi da mai taimaka masa na musamman a vangaren yaxa labarai Malam Garba Shehu ya ce shugaba Buhari ya tafi Saudiyya ne don ya halarci taron qungiyar OIC.

Amma abin da ya xaure wa jama’a kai shi ne yadda shugaban bai halarci walimar cin abincin dare a xakin taro na Banquett Hall da ke fadar shugaban a ranar da aka yi bikin rantsar da shi ba.  Walimar ta samu halartar tsofaffin Ministoci da Jakadu da manyan ’yan kasuwa irin su Aliko Xangote da sarakunan gargajiya da sauransu.

Sai dai da yawa daga cikin ’yan qasa sun ba shugaban   shawarwari a game da yadda ya kamata ya tafiyar da salon mulkinsa a karo na biyu.

Shugaban Kwamitin Kula da ’yan gudun hijira a majalisar wakilai Muhammad Sani Zorro ya shawarci shugaban ne da ya tabbatar ya haxa kai da ’yan jarida a wannan karo da hakan zai sa ya samu nasara a karo na biyu.

Shi kuwa xan takarar shugaban qasa a Jam’iyyar GDPN a zaven da aka yi a ranar 23 ga watan Fabrairun wannan shekara Davidson Akhinmien ya shawarci Buhari ne ya fi mayar da hankali a game da shawo kan matsalar tsaro.

Shi ma shugaban qungiyar masu jefa quri’a ta qasa (VOTAS) Kwmaared Mashood Erubami ya nemi shugaba Buhari ya fi mayar da hankali a game da magance matsalar tsaro da farfaxo da ilimi da kuma samar da ayyukan yi.

Haka kuma da yawa daga cikin ’yan Najeriya sun ba shugaba Muhammadu Buhari shawara a game da matakan da ya dace ya xauka a wannan zango don ganin ya samu nasara.

Buhari dai ya samu nasara ne a zaven shugaban qasra da aka yi a ranar 23 ga watan Fabrairun wannan shekara bayan ya samu fiye da quri’u Miliyan 15 inda ya kayar da abokin hamayyarsa Atiku Abubakar wanda ya samu kimanin quri’u miliyan 12.

Hakan ya sa aka sake rantsar da shi a shekaranjiya Laraba don ci gaba da mulki a karo na biyu.

 

Varayi sun ci kasuwa a bikin rantsar da Gwamna Badaru

A Jihar Jigawa, wakilinmu Umar Aqilu Majeri ya ruwaito yadda varayin wayoyin hannu da kuma ’yan sane suka ci karensu babu babbaka a bikin rantsar da Gwamna Muhammad Abubakar Badaru a karo na biyu tare da  Mataimakinsa wanda a baya tsohon Kwamishinan kuxi ne Malam Umar Namadi Kafin Hausa.

Varayin da ’yan sanen sun samu damar aikata haka ne saboda yadda dubban jama’a suka yi cincirindon halartar bikin rantsar da Gwamnan.

Wakilinmu ya ji yadda mutanen da aka yi wa sata suka riqa yin qorafi. Wasu sun ce an sace masu wayoyinsu ne  a aljihu yayin da wasu suka koka a game da yadda aka yi amfani da reza wajen sace musu kuxaxen da ke aljihunsu ba tare da sani ko kama waxanda suka aikata hakan ba.

Gwamna Badaru a jawabinsa ya nemi al’ummar jihar su sake ba shi cikakken haxin kai da goyon baya don ganin ya ci gaba da aiwatar da ayyukan ci gaba ga al’umma.

Mai Shari’a Sabo Wada Ringimi ne ya rantsar da Gwamna Badaru da sabon mataimakinsa Umar Namadi Kafin Hausa kasancewa Mataimakinsa na da Ibrahim Hassan Haxeja ya zama Sanata.

 

Gwamna Tambuwal ya karbi rantsuwa a wa’adin mulkinsa na biyu

A Jihar Sakkwato kuwa wakilinmu Nasiru Bello Sakkwato ya ruwaito Gwamnan Jihar Alhaji Aminu Waziri Tambuwal an sake rantsar da shi a wa’adin mulkinsa karo na biyu.

A jawabin da ya yi wa Sakkwatawa ya ce yau (shekaranjiya Laraba) wata rana ce ta murna a gwamnatin dimukuraxiyya bayan an sake rantsar da shi a karo na biyu.

Xaruruwan Sakkwatawa ciki har da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’a ne suka halarci bikin rantsar da Gwamna Tambuwal da mataimakinsa a shekaranjiya Laraba.

Jim kaxan da rantsar da shi ne Gwamnan ya yi jawabi mai ratsa zukata inda ya xauki alqawarin xorawa a kan ayyukan da ya faro kuma zai tafi da kowane vangare ba tare da nuna fifiko ba.

 

Sarki Sanusi bai halarci bikin rantsar da Ganduje ba

Rahotannin da ke fitowa daga Jihar Kano sun nuna Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi na biyu bai halarci bikin rantsar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a karo na biyu ba.

Sai dai rahotanni sun nuna Sarkin bai halarci bikin rantsar da Gwamna Ganduje ba ne saboda dambarwar sake qirqiro sababbin masarautu da gwamnatin Ganduje ta yi da hakan ta sa dangantaka ta yi tsami a tsakain Gwamnan da Sarki Sanusi. Sai dai bayanan sirri sun nuna jami’an tsaro ne suka shawarci Sarkin da kada ya halarci bikin rantsarwar don kaucewa yiwuwar tashin hankali.

Gwamna Ganduje ya yi alqawarin ci gaba da muhimman ayyukan raya jihar da ya faro a wa’adin mulkinsa na farko.

 

Tari ya hana Gwamnan Borno karanta jawabi

Daga Jihar Borno, rahotanni sun ce an samu nasarar rantsar da sabon Gwamnan Jihar Farfesa Baba Gana Umara Zulum a shekaranjiya Laraba.

An rantsar da Gwamnan ne tare da mataimakinsa a gaban dubban jama’a da suka yi tururuwa don ganin yadda bikin rantsar da sabon gwamnan za ta kasance.

Sai dai a lokacin da Gwamna Baba Gana Umara Zulum yake karanta jawabinsa ne sai tsananin tari ya sarqe shi. Ya xauki tsawon lokaci yana tarin babu qaqqautawa da hakan ya tayar da hankalin al’umma.

Daga nan jami’an tsaro suka shawarci gwamnan da ya zauna na wasu mintuna don ya huta.

Rahotanni sun ce bayan ya zauna na kimanin minti biyar sai ya sake miqewa don ci gaba da karanta jawabi amma sai matsanancin tarin ya sake dawo masa.  Nan take aka xage taron bayan an gudanar da taken Najeriya inda daga nan sabon gwamnan da tsohon Gwamna Kashim Shettima suka bar filin.

A taqaitaccen bayanin Gwamnan ya yi alqawarin aiwatar da muhimman abubuwa 10 da gwamnatinsa ta tsara da suka haxa da samar da tsaro da ayyukan yi da bunqasa ilimi da noma sauransu.

Sai dai rahotanni sun ce Gwamnan ya fara tarin ne saboda barkonon tsohuwar da wani jami’in xan sanda ya harba saboda cunkoso.

Gwamnan ya kasance na bakwai a jerin Gwamnonin farar hular da suka mulki Jihar Borno.

El-rufa’i zai xauki matakai masu tsauri don bunqasa Kaduna

Daga Jihar Kaduna wakilinmu Andrew Agbese ya ruwaito yadda aka rantsar da Gwamna Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i a karo na biyu a shekaranjiya Laraba.

An rantsar da Gwamnan ne tare da Mataimakiyarsa Dokta Hadiza Sabuwa Balarabe.

Dokta Hadiza Balarabe ta kasance mace ta farko a tarihin Jihar Kaduna da ta zama Mataimakiyar Gwamna.

Dubban jama’a ne suka yi tururuwa Dandalin Murtala da ke Kaduna don ganin yadda bikin rantsarwar ta kasance.

A jawabinsa Gwamna Malam Nasir ya ce zai xauki matakai masu tsauri a wajen tafiyar da mulkinsa a karo na biyu da hakan zai ciyar da jihar gaba a fannoni da dama da suka haxa da samar da tsaro da bunqasa tattalin arzikin jihar da sauransu.

 

Za a fara haqar man fetur a Jihar Kebbi

Wakilinmu Isma’il Adebayo daga Jihar Kebbi ya ruwaito Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na Jihar ya bayar da tabbacin an kusa fara haqar man fetur a Jihar nan da qanqanen lokaci.

Gwamnan ya faxi haka ne a jawabinsa jim kaxan bayan an rantsar da shi a matsayin Gwamnan Jihar a karo na biyu a shekaranjiya Laraba.Gwamnan ya ce gwamnatin jihar da kamfanin NNPC ne za su haxa gwiwa wajen fara haqar man fetur a jihar. Gwamnan ya ce kwanan nan za a qaddamar da kamfanin sarrafa tumatir da na sarrafa shinkafa da sauransu.

An yi bikin rantsar da Gwamnonin ne a Jihohi 29 da ke faxin qasar nan yayin da wasu sababbin Gwamnoni ne a Jihohi irin su Bauchi da Gombe da Borno da Yobe, wasu gwamnonin kuwa sun koma ne a karo na biyu irin su Gwamnan Jihar Kano da na Kaduna da Sakkwato da Kebbi da Filato da sauransu.