✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ruftawar gini ta kashe mutum 4 a Legas

A yanzu dai adadin mutanen da muka ceto a raye sun kai uku.

Akalla mutum hudu ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon ruftawar wani ginin bene mai hawa uku a yankin Mushin da ke Jihar Legas.

Hankula dai sun tashi tun bayan rushewar ginin a titin Oyesonuga daura da shataletalen Oye da ke hanyar Isolo a birnin na Ikko.

Tuni dai masu ba da agajin gaggawa suka shiga kai-komo inda kawo yanzu sun ceto mutum hudu daga baraguzon ginin,

Wakilinmu ya ruwaito cewa, jami’an Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA da na takwararta ta Jihar Legas (LASEMA) ne ke aikin ceton hadi da jami’an kwana-kwana da ’yan sanda.

Babban Sakataren LASEMA, Dokata Olufemi Oke-Osanyintolu, ya shaida wa wakilinmu cewa, “da kyar muka ceto wata mace daya a baraguzon ginin bayan an shafe tsawon lokaci ana kai-kawo.

“A yanzu dai adadin mutanen da muka ceto a raye sun kai uku, kuma an ba su kulawar gaggawa tun kafin a garzaya da su asibiti.

“Mun zakulo gawarwakin mutum hudu, maza biyu da mata biyu.

Ana ci gaba da aikin ceto yayin hada wannan rahoto.