Akalla mutum ne 23 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 70 suka jikkata daren Litinin sakamakon ruftawar wata gadar jirgin kasa mai hanyar sama a Kudancin birnin Mexico.
Magajin garin birnin Mexico, Claudia Sheinbaum, ya ce hatsarin ya auku ne yayin da wani ginin kankare ya rufta a kan gadar yayin da jirgin kasan ke tafiya a kanta.
Claudia ya ce, “abin bakin ciki mutum 23 ne suka rasa rayukansu, ciki har da yara.
“A halin yanzu, ana ci gaba da aikin ceto kuma za a gudanar da bincike domin gano musabbabin aukuwar hadarin,” a cewarsa.
Mahukunta a ranar Talata sun sanar da cewa nan take aka garzaya da mutum 49 daga cikin wadanda suka jikkata zuwa asibiti.
Hoton bidiyon da wani gidan talabijin na yankin ya hasko ya nuna yadda tarragon jirgin ke reto a jikin gadar sarkake cikin wasu wayoyi na karfe, inda goshin jirgin ke kallon kasa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, a shekarar 2012 ce aka fara amfani da gadar jirgin kasa ta Metro 12.