✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rufe Kwalejojin Tarayya zai zamo nasara ga ’yan ta’adda

A makon jiya ne wani mukarrabin Minista a Ma’aikatar Ilimi Mista Nyeson Wike ya ba da sanarwar cewa gwamnati ta amince da rufe kwalejojin Gwamnatin…

A makon jiya ne wani mukarrabin Minista a Ma’aikatar Ilimi Mista Nyeson Wike ya ba da sanarwar cewa gwamnati ta amince da rufe kwalejojin Gwamnatin Tarayya biyar da aka fi sani da Kwalejojin Hadaka da suke sassan jihohin Arewa maso Gabas. Kwalejojin suna jihohin Adamawa da Borno da Yobe ne.

 daukar matakin na gwamnati ya biyo bayan kisan rashin imani ne da wasu da ake zargin ’yan Boko Haram ne suka yi wa kusan dalibai 60 a Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Buni Yadi da ke Jihar Yobe a makon shekaranjiya lamarin da samu mummunar la’anta a cikin gida da waje.  
Jihohin uku suna karkashin dokar ta-bacin da Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kakaba musu a bara na tsawon wata shida a karon farko da niyyar dakile hare-haren ’yan ta’adda  da dakatar da zubar da jini da lalata dukiya. Kuma an sake kara mata wa’adin wata uku saboda sojojin da aka tura can sun gaza cimma nasarar abin da ya kai su.
Ba wannan ne karo na farko ba da mahara suke kai irin wannan hari ga kwalejisu yi ta’asa a Buni Yadi ba.
A Yunin bara maharan sun kai hari ga Makarantar Sakandaren Gwamnatin jiha a garin Damaturu fadar Jihar Yobe, inda suka kashe dalibai takwas da malaminsu daya. Watan bayan wata daya maharan sun kai hari ga wata Makarantar Sakandare Gwamnati a garin Mamudo a Jihar Yobe inda suka kashe dalibai 29. Kuma a Satumban da ya gabata, sun kai hari ne ga Kwalejin Aikin Gona da ke garin Gujba a Jihar Yoben suka kashe dalibai 40.
Duk da matakan dokar ta-baci da kirkiro rundunar soja da tura karin sojoji zuwa yankin, masu gudanar da wadannan kashe-kashe ga alama suna samun damar yawo kai-tsaye cikin jerin motoci  dauke da miyagun makamai yankuna da dama na shiyyar kamar yadda rahotanni da su kansu hukumomin sojojin suke tabbatarwa ba tare da an kalubalance su ba.
Maharan sun kuma rika kai hare-hare tare da kone garuruwa da kauyuka inda suka hallaka mutane da dama tare da kone gine-ginen gwamnati da na jama’a.
Sakamakon harin Kwalejin Hadaka na Buni Yadi na watan jiya ne mahukuntan tarayya suka bayyana wa jama’a niyyarsu ta daukar matakin rufe makarantun da ke yankin. Kuma lura da akidar Boko Haram na haramta ilimin zamani lamarin da ya sa suke kai hari ga makarantun boko, duk wani yunkuri na daukar irin wannan mataki zai zamo rashin kyakkyawan tunani.
Umarnin Gwamnatin Tarayya na rufe makarantun hadakar a yankin mace ce da ciki da ba san abin za ta haifa ba, akalla dai kamar an amince cewa ba za a iya bayar da kariya ko mu ce tsaro ga yankunan da aka tura dubban jami’an tsaro domin su bayar da tsaron ke nan ba.
Amincewa da wannan gazawa ta irin wannan hanya na rufe makarantu na nufin ’yan ta’adda sun samu nasara, sun cimma burin akidarsu. Tabbas ba wannan ne sakon da gwamnati ke niyyar aikewa ta daukar wannan mataki ba; to amma shi ne ainihin abin da ya faru.  
Gwamnatin Jihar Yobe ta samu yabo a bara lokacin da ta ki mika wuya ga manufar ’yan ta’addar, musamman bayan harin Gujba. Abu ne mai daci, kuma mai tsadar dauka, to amma illar dogon lokaci da zai haifar bai kamata a kawar da kai daga gare shi ba. A wannan bangare an samu nasara kan ’yan ta’addar.
Bai kamata Gwamnatin Tarayya ta dauki saukakkiyar hanya ta rufe makarantun ba, ta bar iyaye da nauyin nemo guraben karatu ga ’ya’yansu da za a sallama daga makarantun ba idan aka aiwatar da umarnin.
Mika wuya ga farfagandar ’yan ta’addar maimakon yakar manufarsu ta hanyar samar da tsaro ga daliban zai yi mummunar illar ga kasar nan da kuma yakin da ita kanta gwamnati ke yi da maharan.
Yanzu da ta bayyana jami’an tsaro sun tasa maharan a gaba gadan-gadan, bayan harin Buni Yadi, zai zamo mika wuya a ruwan sanyi ga ’yan ta’addan idan gwamnati ta ci gaba da aikin da wannan muguwar shawara.