An samu wani sabon rudani a hedkwatar jam’iyyar APC ta kasa bayan da Mataimakin Sakatarenta, Victor Giadom, ya ayyana kansa a matsayin Mukaddashin Shugaba, sannan ya soke hukuncin kwamitin tantance masu son tsayawa takara a zaben gwamnan Edo.
Hakan na zuwa ne dai sa’o’i bayan Sakataren Yada Labarai na Kasa, Lanre Issa-Onilu, ya bayyana nadin Mataimakin Shugaba na Kasa daga Kudu Ajibola Ajimobi a matsayin mukaddashin shugaban jam’iyyar, bayan da Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin dakatar da Adams Oshiomhole.
Mista Giadom, wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya kira a hedkwatar jam’iyyar ranar Laraba, ya ce ya yanke wannan shawara ne bisa la’akari da hukuncin da wani alkali ya yanke watanni biyu da suka wuce.
- Jam’iyyar APC ta nada Ajimobi ya zama shugabanta
- Gwamnan Edo ya fice daga APC bayan ganawa da Buhari
- APC ta hana gwamnan Edo tsayawa takara
“Jiya Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa Kwamared Adams Oshiomhole daga mukamin Shugaban Jam’iyyar APC na kasa.
“Don haka ne nake jan hankalinku cewa ranar 16 ga watan Maris na 2020, Mai Shari’a S.U. Bature ya ba da umarnin cewa, bayan dakatarwa ta farko da aka yi wa Kwamared Adams Aliyu Oshiomhole, ni Cif Honorebul Victor Giadom na zama Mukaddashin Shugaban Jam’iyya na Kasa.
“Ba a samu damar aiwatar da wannan umarni ba nan take saboda hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke a ranar, wanda ya daga wa Adams Oshiomhole kafa zuwa wani lokaci”, inji Cif Giadom.
Shawara a kan Edo
Ba tare da bata lokaci ba kuma Cif Giadom ya bayyana soke dukkan matakan da Kwamared Oshiomhole ya dauka na shirya zaben fitar da gwani a jihar Edo.
“A matsayina na Mukaddashin Shugaban Jam’iyyarku kuma shugaban Kwamitin Gudanarwa na Jam’iyyar, na soke hukuncin kwamitin tantance masu son tsayawa takarar gwamna a jihar Edo da na kwamitin sauraren korafe-korafensu wadanda tsohon shugaban jam’iyya ya kafa.
“Mun dauki wannan mataki ne bisa dogaro da tanade-tanaden Kundin Tsarin mulkin Najeriya, wanda ya haramta wa duk mai muradi a cikin wani lamari ya yanke hukunci a kai”, inji Cif Giadom.
Daga nan ya ce za a sake aikin tantance masu son tsayawa takarar a tsakanin ranakun Laraba da Alhamis.
“Don haka muke kira ga dukkan masu son shiga zaben fitar da gwani a jihar Edo da su zo a sake tantance su tsakanin yau da gobe”, inji shi.
Matsayin Obaseki
Ya kuma yi kira ga dukkan ’yan jam’iyyar masu son tsayawa takara da kada su fice, yana mai tabbatar da cewa za a yi musu adalci.
Kwamitin tantance masu son shiga zaben fitar da gwanin dai ya haramta wa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, da wasu mutum biyu, shiga zaben fitar da gwanin da jam’iyyar za ta yi,
Dangane da hikincin da ya yanke a kan gwamnan, kwamitin ya kafa hujja da cewa akwai tufka da warwara game da sakamakon jarrabawar Mista Obaseki.
Tuni dai Gwamna Obaseki ya ba da sanarwar ficewa daga jam’iyyar ta APC yana cewa da ma ya san duk wani tsari da Kwamared Oshiomhole ya jagoranta ba zai yi masa adalci ba.
Sai dai kuma babu tabbas a kan ko zai yi amfani da wannan dama ya koma jam’iyyar.
Wasu ’yan jam’iyyar daga jihar Edo ne dai suka shigar da kara suna bukatar a dakatar da Kwamared Oshiomhole daga mukamin shugaban APC na kasa, bukatar da wata kotun Yankin Babban Birnin Tarayya ta biya musu, amma Kotun Daukaka Kara ta jingine hukuncin.