✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Roy Hodgson ya zama kocin Cystal Palace

A shekaranjiya Laraba ne kulob din Crystal Palace ya bayar da sanarwar nada tsohon kocin Ingila Roy Hodgson a matsayin sabon koci. dan shekara 70…

A shekaranjiya Laraba ne kulob din Crystal Palace ya bayar da sanarwar nada tsohon kocin Ingila Roy Hodgson a matsayin sabon koci.

dan shekara 70 Hodgson ya zama sabon kocin kulob din ne bayan an kori tsohon koci Frank De Boer a ranar Litinin da ta wuce.

Kulob din ya sallami De Boer ne bayan ya kwashe kwanaki 77 kacal yana horar da ’yan wasan kulob din amma ganin yadda ya jefa kulob din cikin matsala a kakar wasa ta bana, inda kawo yanzu kulob din ya rasa dukkan wasanninsa uku da ya yi ba tare da zura kwallo ko daya a raga ba, ta sa kulob din yanke shawarar rabuwa da shi.  Wannan shi ne sakamako mafi muni da kulob din Palace ya samu a gasar firimiyar Ingila tun bayan shekara 93.

Sabon koci Hodgson ya sanya hannu ne a kan kwantaragin shekara biyu a kan Fam miliyan biyu kuma an nuna zai samu garabasar Fam Miliyan 1 idan ya yi kokari a gasar rukunin firimiyar Ingila a bana.