✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rooney ya yi ritaya daga yi wa Ingila kwallo

A shekaranjiya Laraba ne shahararren dan kwallon Ingila Wayne Rooney ya yanke shawarar daina yi wa kasarsa Ingila kwallo.  Ya ce ya dauki wannan mataki…

A shekaranjiya Laraba ne shahararren dan kwallon Ingila Wayne Rooney ya yanke shawarar daina yi wa kasarsa Ingila kwallo.  Ya ce ya dauki wannan mataki ne ba tare da bata wani lokaci ba, kuma hakan na nuna ya kawo karshen tsawon lokacin da ya dauka yana yi wa Ingila wasa.

Wayne Rooney wanda a kwanakin baya ya canza sheka daga kulob din Manchester United zuwa na Eberton ya buga wa Ingila wasanni sau 119 kuma ya samu nasarar zura kwallaye 53 a raga.

Hukumar shirya kwallon kafa ta Ingila (FA) ta tabbatar da yin ritayar Rooney daga yi mata kwallo a lokacin da kocin kungiyar ya nemi ya sanya sunansa a daya daga cikin ’yan kwallon da za su buga wa Ingila wasa da kasashen Malta da Slobakia.

Yanzu dai ta tabbata dan kwallon ba zai halarci gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a badi idan Allah Ya kaimu ba.