Tsohon dan kwallon kafar Brazil Ronaldo Nazario Luis de Lima ya samu nasarar mallakar kashi 51 daga cikin 100 na kulob din Real balladolid da ke Sifen kamar yadda rahotanni daga kulob din suka tabbatar.
A lokacin da kulob din yake gabatar da Ronaldo ga magoya bayansa a ranar Litinin da ta wuce, Ronaldo ya ce ya yi murnar kasancewa mutumin da ya fi kowa mallakar hannun jari a kulob din kuma zai yi kokarin ganin ya daukaka martabar kulob din a Sifen da ma a duniya baki daya.
Ronaldo ya ce, ya amince shugaban kulob din na yanzu Carlos Suarez ya ci gaba da zama a mukamin shugaban kulob din yayin da shi kuma zai rike mukamin shugaban majalisar gudanar da kulob din.
“Zan yi amfani da kwarewa da basirata wajen gudanar da harkokin kulob din a bisa turbar gaskiya da rikon amana. Kuma zan yi duk maiyiwuwa na ga na dora kulob din a hanya madaidaiciya don yin gogayya da kowane kulob a fadin duniya”, inji shi.
Ronaldo wanda ya taba lashe kyautar Gwarzon dan kwallon duniya sau uku, ya bugawa kulob da dama wasa ciki har da Real Madrid da FC Barcelona na Sifen da kuma Inter Milan na Italiya kafin ya daina kwallo a shekarar 2011.
Kafin yanzu ya mallaki hannayen jari a kungiyoyin kwallon kafa da dama a Brazil da kulob din tseren mota da kamfanonin da ke sarrafa kayayyakin wasanni a kasashen Amurka da China da kuma Brazil.