✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo ya lashe Gwarzon dan kwallon duniya a karo na hudu

Shahararren dan kwallon Fotugal da ke buga wa kulob din Real Madrid na Sifen kwallo ya zama Gwarzon dan kwallon duniya a karo na hudu.…

Shahararren dan kwallon Fotugal da ke buga wa kulob din Real Madrid na Sifen kwallo ya zama Gwarzon dan kwallon duniya a karo na hudu.

A ranar Litinin da ta wuce ne aka sanar da dan kwallon a matsayin Gwarzon dan kwallon duniya na bana.
dan kwallon ya samu nasara ne bayan ya doke abokan takararsa Lionel Messi, dan kwallon FC Barcelona na Sifen da kuma Antoine Griezmann dan kwallon Atletico Madrid shi ma a Sifen.
dan kwallon wanda ya taba lashe wannan gasa a shekarar 2008 da 2013 da kuma 2014 ya samu nasara a wannan karo ne bayan ya taimaka wa kasar haihuwarsa Fotugal lashe kofin Nahiyar Turai (Euro) a kakar wasan da ta wuce da kuma yadda ya taimaka wa kulob din Real Madrid na Sifen lashe kofin zakarun kulob din Turai (Champions League) a karo na 11 a kakar wasan da ta wuce.
Wadannan nasarori da Ronaldo ya samu ne suka ba shi damar zama Gwarzon dan kwallon duniya na bana.
Lionel Messi wanda ya taba lashe gasar sau biyar shi ne ya zo na biyu bayan ya taimaka wa kulob din FC Barcelona lashe kofuna biyu a kakar wasan da ta wuce. Sai dai bai samu nasarar lashe kofin Kudancin Amurka (Copa America) ga kasar Ajantina ba, bayan Chile ta lallasa su a bugun fanariti a wasan karshe.
Shi kuma Antoine Griezmann dan kwallon Atletico Madrid ya zama na uku ne bayan ya taimaka wa kulob din Atletico Madrid na Sifen kai wa wasan karshe a gasar zakarun kulob na Turai (Champions League) a kakar wasan da ta wuce. Sannan ya taimaka wa kasar haihuwarsa Faransa kai wa wasan karshe a gasar Nahiyar Turai (Euro) bayan Fotugal ta samu nasara a kansu a wasan karshe a bugun fanariti.