✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo ya fara tunanin komawa Chelsea

Shahararren dan kwallon Real Madrid da ke Sifen Cristiano Ronaldo ya nuna sha’awar komawa kulob din Chelsea na Ingila a karshen kakar wasa ta bana.…

Shahararren dan kwallon Real Madrid da ke Sifen Cristiano Ronaldo ya nuna sha’awar komawa kulob din Chelsea na Ingila a karshen kakar wasa ta bana.

dan kwallon wanda ya dade da nuna vacin ransa ga mahukunta Sifen wajen yi masa kagen ba ya biyan haraji, ya ce ya fara tunanin komawa tsohon kulob dinsa na Manchester United ne amma ganin yadda Manchester ta nuna ba ta sha’awarsa a yanzu ta sa ya yanke shawarar komawa Chelsea.

Rahotanni da ke fitowa sun nuna dan kwallon yana son barin kulob din Madrid saboda yadda Madrid ta dage wajen sayo dan kwallon Chelsea Eden Hazard da hakan bai yi masa dadi ba.

Masana harkar kwallo suna ganin Ronaldo zai iya barin Madrid a karshen kakar wasa ta bana ganin yadda tauraruwarsa ta fara dusashewa a kakar wasa ta bana.