✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo ne dan kwallon kafa na duniya karo na 5

Dan wasan Realmadrid da kasar Portugal Cristiano Ronaldo ya sake lashe gasar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya wanda ake kira Ballon Do’Or karo…

Dan wasan Realmadrid da kasar Portugal Cristiano Ronaldo ya sake lashe gasar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya wanda ake kira Ballon Do’Or karo biyar.

Wannan nasarar da Ronaldo ya samu, ta sa ya yi kankankan da Messi, wanda shi ma ya lashe gasar sau biyar.

Ronald da Messi dai sun fi kowa kafa tarihi a wasan kwallon kafa a tarihin wasan. Kuma yanzu haka sun kwashe sama da shekara 10 suna lashe gwarzon dan wasan na shekara-shekara.

Hukumar kwallon kafa ta Faransa c eta kasancewa tana bayar da kyautar. A shekarar 2008 sai suka hada gwiwa da Hukumar FIFA suka ci gaba da bayar da kyautar. Sai kuma bara suka rabe, inda FIFA ta fara bada na ta kyautar ta gwarzon dan wasa da ‘yar wasa.

Cristiano Ronaldo dai shi ne ya lashe gasar ta FIFA sai biyu a jere. Sai kuma kyautar wanda ya fi zura kwallaye a yankin Turai (European Golden Boot/Shoe), wanda Ronaldo da Messi suke hudu hudu. Sai kuma kyauta gwarzon dan kwallon kafa na yankin Turai, wanda Ronaldo ya lashe sau uku, shi kuma Messi sau biyu.

Haka kuma Ronaldo ya taba zama wanda ya fi zura kwallaye a gasar cin kofin zakarun kungiyoyin Turai, wanda ake wa lakabi da gasar gwanaye sau shida, shi kuma Messi sau biyar. Sai kuma na Laliga kuma da suka lashes au hudu hudu.