✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldinho zai yi takarar Sanata a Brazil

A makon jiya ne fitaccen dan kwallon nan duniya Ronaldinho ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar Sanata a kasarsa  ta haihuwa Brazil.  Kamar yadda rahotanni…

A makon jiya ne fitaccen dan kwallon nan duniya Ronaldinho ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar Sanata a kasarsa  ta haihuwa Brazil.  Kamar yadda rahotanni suka nuna, tuni tsohon dan kwallon na FC Barcelona na Sifen da AC Milan na Italiya ya yanki fom don ganin an fafata da shi a takara idan zaben ya zo.

A bara ne aka kalato dan kwallon ya yanke shawarar shiga harkokin siyasa, inda ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takarar Sanata.

Ana sa zan za a yi zaben ne a watan Oktoban bana.

Rahoton ya ce tsohon dan kwallon zai yi takarar ce a karkashin Jam’iyyar Brazil Republican Party (BRP).

Rahoton ya kara da cewa, tsohon dan kwallon mai shekara 38 cika tare da ya mayar da fom din yin takarar ga jam’iyyarsa inda shugabannin jam’iyyar suka karbe shi da hannu bibbiyu.

A lokacin da yake jawabi a hedkwatar Jam’iyyar BRP, Ronaldinho ya ce “Ina mai matukar farin ciki da Allah Ya nuna mini wannan rana a kokarin da nake yi na tsayawa takarar  Sanata.  Ina fata idan na samu nasarar hawa kujerar, zan bayar da gudunmawata wajen kawo ci gaba a kasar haihuwata.”

A  jawabin, Shugaban Jam’iyyar BRP, Sanata Eduardo Lopes ya yaba da shawarar da tsohon dan kwallon ya yanke ta tsayawa takara a karkashin Jam’iyyar BRP.  Ya ce ko shakka babu Ronaldinho zai bayar da gudunmawa a bangaren siyasa kamar yadda ya bayar wajen daukaka martabar kasar Brazil a bangaren kwallon kafa.

Idan za a tuna tsohon dan kwallon Brazil Romario ya taba zama Sanata bayan ya shiga harkokin siyasa.

Al’amarin tsayawa takara ga tsofaffin ’yan kwallon kafa a sassan duniya ba sabon abu ba ne, domin a bana an zabi tsohon dan kwallon Laberiya, George Weah a matsayin Shugaban kasa matsayin da babu wani dan kwallon kafa da ya taba rikewa a duk duniya.