✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Romon dimokuradiyyar Gwamnatin Shugaba Buhari

Tabbas tun ran gini ran zane, hakika kowa ya ga kamun ludayin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. Domin tun daga ranar 29 ga Mayun da ka…

Tabbas tun ran gini ran zane, hakika kowa ya ga kamun ludayin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. Domin tun daga ranar 29 ga Mayun da ka dare karagar mulkin kasarmu ta fara sauya alkibila daga hagu zuwa dama. Da farko da makwabta aka fara ziyarar nemo mafita daga matsalar Boko Haram. Ziyararka a Jamhuriyar Nijar da Kamaru da Chadi da Binin ta tabbatar da neman hadin kai da inganta tsaron nahiyarmu baki daya da habaka tattalin arzikinmu, uwa uba gayyatarka zuwa Amuruka da taron G7.
A kwana 100 nan wallahi har wutar lantarki ta canja. Domin kuwa babu ranar da ba a samunta awa tara. Al’amarin yaki da rashawa ya kankama, barayin kasa masu almundahana da dukiyar Najeriya sun fara shiga taitayinsu. Lokaci kadan Shugaban ya ce mu ba shi don kwato wa al’umma dukiyarsu, mun yi na’am da hakan.
Domin ko rundunar sojin kasa da ka yi wa kwaskwarima, yanzu ta san inda aka dosa da yaki da masu ta da kayar baya, ba yaudara da karya a ciki. Muna addu’ar Allah Ya taimaki Gwamnatin Buhari ya haskaka mana kasarmu. Talakawa mu ci ribar romon dimokuradiyya.
Hafizu Balarabe Gusau ya rubuto daga Jihar Zamfara 07035304499.