Gwamnatin Romania ta yi tayin bai wa daliban Najeriya damar ci gaba da karatu a jami’o’in kasar bayan sun tsere daga Ukraine sakamakon yakin da ake tafkawa a kasar.
Babban Sakatare a Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Gabriel Aduda, ya ce Sorin Cimpeanu, Ministan Ilimi na Romania wadda makociyar Ukraine ce, shi ne ya bayyana hakan.
Mista Aduda ya kara da cewa yanzu haka sun soma tattaunawa da sauran makotan kasashe kamar Poland da Hungary da Girka don su bai wa ‘yan Najeriya irin wannan damar.
‘Yan Najeriya kusan 2,000 ne aka tabbatar sun tsallaka kasashe makotan Ukraine a yunkurinsu na samun mafaka daga yakin da aka fara fafatawa ranar 24 ga watan Fabarairu.
Tuni aka kwaso ‘yan kasar kusan 1,000 amma har yanzu akwai dalibai a yankin Sumy na Ukraine da ke neman tallafin gwamnati don su koma gida.