Roma na tattaunawa da Chelsea kan ɗauko aron ɗan wasan gaba, Romelu Lukaku a kakar wasa ta bana.
Tattaunawar da ke matakin farko na iya kasancewa mafita ga kungiyar ta Serie A da yanayin da Lukaku, mai shekara 30, da Chelsea suka samu kansu a ciki.
- Ranar Hausa ta Duniya: Waiwaye kan sunayen Bahaushe da kuma fa’idojinsu
- Matatun man fetur 4 za su fara aiki a Najeriya a badi — Minista
Lukaku, wanda ya shafe kakar wasa ta bara a zaman aro a Inter Milan, bai taka leda ba a shirye-shiryen Chelsea na tunkarar kakar wasa ta bana ba, kuma yana atisaye ba tare da kungiyarsa ta farko ba.
Kocin Roma Jose Mourinho ya horas da Lukaku a Chelsea da Manchester United.
Kocin Chelsea Mauricio Pochettino ya san shirin kungiyar na sayar da ɗan wasan gaban Belgium ɗin a lokacin da ya karɓi aikin Stamford Bridge a watan Yuli.
Chelsea na sa ran za ta warware makomar Lukaku kafin karshen kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ta Turai a ranar 1 ga watan Satumba.
Ba a tsammanin za a aiwatar da yarjejeniyar cikin sauri ba, kuma ana la’akari da zaɓin sayar da Lukaku ga wata kungiya a Saudiyya idan aka sami masu sha’awar ɗan wasan da ya ke kasuwar saye da sayar da ‘yan wasan da Saudiyya za ta rufe a ranar 20 ga Satumba.